For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kwamitin Samar Da Zaman Lafiya Na Abdussalami Ya Gargadi ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

Kwamitin Samar Da Zaman Lafiya na Kasa, NPC, wanda tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdussalami A. Abubakar (mai ritaya), ya bayyana kin amincewarsa da maganganun tunzura al’umma da wasu masu magana da yawun ‘yan takarkarun shugaban kasa kan yi wajen tallata ‘yan gtakararsu.

Kwamitin ya bayyana cewa, za a zargi ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 da laifin rigingimun da masu magana da yawunsu suka jawo a yayin tunkarar zabe.

A jawabin da Janar Abdussalami, Bishop Matthew Hassan Kukah da Atta Barkindo suka sanya wa hannu, an bayyana siyasar gaba da masu magana da yawun ‘yan takarar shugaban kasa ke yi a matsayin abun kaico.

Idan za a iya tunawa, ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakansu da manyan masu ruwa da tsaki sun hadu makonni da suka gabata domin sanya hannu a yarjejjeniyar tabbatar da zaman lafiya.

Takardar gargadin ta ce wa ‘yan takarar shugaban kasa, “Duk ‘yan takara zasu dau laifin abubuwan da aka fada a madadinsu ko a madadin jam’iyyarsu.”

“Mugayen maganganu da maganganun batanci na rage darajar mutane ne, ‘yan takararsu da kuma jam’iyyarsu. ‘Yan Najeriya su shirya wajen hukunta masu kakalo rigingimu ta hanyar dena kula su da ‘yan takararsu.”

Comments
Loading...