For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kwamitin Tantance Ɗan Takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa Na PDP Ya Amince Da Wike

Wani kwamitin wucin gadi da jam’iyyar PDP ta kafa domin tantance wanda zai mara Atiku Abubakar baya a matsayin ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya amince da Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike a matsayin wanda zai yi takarar.

Kwamitin ya yanke wannan hukuncin ne a jiya Talata bayan zaman tattaunawa da ya sha yi tun bayan kafa shi a makon jiya.

Wike dai ya samu nasarar zamewa ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasar ne bayan amincewar baka da baka da aka gudanar, inda ya samu ƙuri’u 16 cikin 20.

Hukuncin dai ya jawo an ajjiye gwamnoni uku da suke neman takarar tare da Wike, wadanda suka haɗa da Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom) da Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu.

Kwamitin dai na ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Yankin Arewa, Ambasada Umar Damagum.

Sauran mambobin kwamitin sune, Sakataren Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, Sakataren Tsare-Tsare na Ƙasa, Umar Bature, Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue, Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto da Bala Mohammed na Jihar Bauchi.

A dai wannan kwamiti akwai tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido; tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ahmed Makarfi; tsohon Gwamnan Jihar Cross River, Liyel Imoke da tsohon Gwamnan Jihar Niger, Babangida Aliyu.

Suma su Sanatan Abuja Philip Aduda; Shugaban Marassa Rinjaye na Majalissar Wakilai, Ndudi Elumelu; da kuma tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, David Mark suna cikin mambobin kwamitin.

An dai rawaito cewa, a ranar 30 ga watan Mayun da ya gabata, Atiku ya baiwa Wike damar zame masa mataimaki, amma Wike ya ce ya jira shi zai yi tuntuɓa akai tukunna.

An kuma gano cewa, Gwamna Wike ya tuntuɓi Gwamna Ortom kan buƙatar ta Atiku, inda Ortom ɗin ya baiwa Wike shawarar cewa ya karɓi tayin.

Comments
Loading...