For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kwanaki 3 Babu Wanda Ya Mutu Dalilin Korona A Najeriya

A Talatar nan Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta sanar a shafinta cewa mutane da suka mutu dalilin Korona yana nan a 2,723.

Hukumar ta kuma sanar da cewa, an sallami mutane 194,167 wadanda suka kamu da cutar, yayinda mutane 9,389 ke karbar magani a sassa daban-daban na Najeriya.

NCDC ta ce, a Litinin jihar Rivers da ke yankin Kudu maso Kudu ke matsayin ta farko a yawan sabbin da suka kamu da cutar inda take da mutane 33.

Jihar Gombe da ke Arewa maso Gabas ita ke biyewa da wadanda suka kamu mutum 32.

Jihar Lagos da ke a matsayin cibiyar cutar a kasa, ta sami karuwar masu cutar guda 29, yayin da jihar Imo ta samu karuwar mutane 25.

Jihohin Arewa ta Tsakiya, Plateau da Benue duk sun sami mutane tara-tara kowannensu, yayin da jihar Bornon da ke Arewa maso Gabas ta sami mutum 4.

Jihar Kano da ke Arewa maso Yamma ta sami karuwar mutane 3 yayin da jihar Delta da ke Kudu maso Kudu ta sami mutum 1.

Comments
Loading...