For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kwanan Nan CBN Zai Fara Baiwa ‘Yan NPower Bashin Yin Sana’a – Minista Sadiya

Gwamnatin Tarayya ta baiyana cewa ‘yan NPower wadanda suka kammala shirin a Batch A da B da suka kai mutum dubu 300 ne zasu karbi bashi daga Babban Bankin Najeriya, CBN, bayan an koya musu sana’o’i.

Ministar Aiyukan Jinkai, Sadiya Umar Farouk ce ta baiyana hakan a jiya Alhamis a lokacin gabatar da jawabi ga manema labarai na mako-mako wanda ma’aikatun gwamnatin tarayya ke yi fadar shugaban kasa.

Ministar ta baiyana cewa, ma’aikatarta ta shirya shirin sallamar ‘yan NPower ne tare da hadin gwiwa da CBN.

Ta baiyana cewa, mutum dubu 300 ne daga cikin mutum dubu 500 wadanda suka kammala shirin na NPower suka baiyana sha’awarsu ta shiga shirin yayewar da za a yi.

Minista Sadiya, ta kara da cewa, za a bayar da horo na musamman ga mutanen kan sana’o’in hannu sannan CBN ya ba su bashin jari.

Sadiya ta kuma ce, shiri ya riga ya yi nisa domin fara aikin horaswar ga ‘yan NPower, inda ta ce kafin karewar watan Maris mai zuwa za a iya fara bayar da bashin kudin ga wadanda suka karbi horon.

Comments
Loading...