Akwai ƙwararan alamu da ke nuni da cewar, Babban Bankin Najeriya, CBN, ya shirya domin ɗaukar matakan farfaɗo da darajar naira a ƴan kwanaki masu zuwa kaɗan.
Wannan ci gaba dai idan ya tabbata, ana sa ran zai jawo faɗuwar farashin dala a kan naira wanwar, abun da kuma zai jawo gagarumar asara ga waɗanda ke da daloli a tare da su.
Mai Riƙon Muƙamin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Folashodun Shonubi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, jim kaɗan bayan ya gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa, Villa, Abuja.
KARANTA WANNAN: Kwanannan Za A Koma Siyar Da Litar Fetur Naira 720 Saboda Faɗuwar Darajar Naira
Shonubi ya ce, ran shugaban ƙasa ya matuƙar ɓaci game da aiyukan masu surutai, abun da ya yarda a matsayin mai ƙara rura wutar tashin farashin dala a kan naira.
A yanzu dai haka ana canja dala 1 ne a kan naira 950 a kasuwannin bayan fage, abun da ake tsoron cewa, zai ƙara tsadar farashin man fetur wanda aka dogara da canjin kuɗi wajen shigo da shi Najeriya.
Wannan kuma na zuwa ne, bayan Gwamnatin Tarayya ta janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu, abun da ya jefa rayuwar mafi yawan ƴan Najeriya cikin ƙunci da talauci.
Shugaban na CBN ya ce, sun tattauna da shugaban ƙasa kan abubuwan da za a yi wajen farfaɗo da darajar naira waɗanda suka haɗa da samar da ƙarin yawan dala a kasuwanni.