For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Kwankwasiyya Za Ta Iya Rasa Wasu Jiga-Jigai Da Zasu Koma Tsagin Shekarau

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Mu’az Magaji wanda aka fi sani da Dansarauniya, ya kyankyasa samun wasu sababbin shiga cikin APC.

Injiniya Mu’az Magaji ya fito shafinsa na Facebook a ranar Juma’ar da ta wuce ya na cewa wasu jagororin bangaren Kwankwasiyya, su na shirin shiga jam’iyyar APC.

Magaji ya ce tsaginsu na G7 wanda Malam Ibrahim Shekarau ke jagoranta zai kara yawa a yayin da suke sauraron shigowar wasu manyan ‘yan adawa.

Daga cikin wadanda za su tsallako zuwa bangaren G7 a cewar tsohon kwamishinan akwai Dr. Yunusa Dangwani, Aliyu Madakin Gini, da kuma Dr. Yusuf Danbatta.

Sai Hon. Nuhu Danburam, Umar Kuliya, Aminu Dala, Zainab Abdu Bako. Akwai su Garba Diso, Sani Rogo, Abdullah Ajiya da wasu da Kwankwasiyya ta ke ji da su.

(Legit Hausa)

Comments
Loading...