A yau Laraba ne dai Sanata Mallam Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano, ya karbi katin jam’iyyar NNPP. Haka kuma ya bada sanarwar fita daga jam’iyyar APC.
Bayan Shekarau ya karbi katin jam’iyyar NNPP, tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin tutar jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya mikawa Sanata Shekarau fom na takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.
An rawaito cewa, an samu jituwa da amanar yin aikin siyasa a tsakanin Shekarau da Kwankwaso.
Babbar manufar haduwar ita ce: a hada karfi da karfe domin a ceto al’ummar Kano da Najeriya daga halin da shiga na rububi da rashin alkibla, kamar dai yanda wata majiya a NNPP ta nuna.
Kafin wannan dai, an gaza daidaita sabanin siyasa tsakanin gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da tawagar ‘yan G7.
Duk masu fada aji na Kano a siyasa da sarauta da kasuwanci da harkar addini, sun saka baki, amma lamarin sasancin ya faskara.
Gwamna Ganduje da shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Hon. Alasan Ado Doguwa da mataimakin gwamnan Kano Dr Nasiru Gawuna sun ziyarci Sardaunan Kano har gida, amma ba a daidaita ba.
Haka kuma sau biyu, tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, yana ziyartar Mallam Shekarau har gida, kuma a karshe sun fuskanci juna.
Mallam Ibrahim Shekarau da shi aka kafa APC a 2013, amma shugabancin APC na lokacin da na yanzu suka gaza warware korafin da Shekarau ya gabatar.