Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jagorantar wani gagarumin taro na wasu manyan siyasar Najeriya karkashin wani yunkuri mai suna The National Movement TNM.
Fitattun mutane da ƴan siyasa da suka halarci taron sun haɗa da Alhaji Tanko Yakasai da Capt Idris Wada tsohon gwamnan Kogi da Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.

A jawabin Kwankwaso ya ce wasu ƴan Najeriya ne da suka damu da abin da ke faruwar suka haɗa kai don ceto ƙasar daga mawuyacin halin da ta shiga.
Ya ce yunƙuri ne na ƴan Najeriya masu kishi da suke zaune a gida da kasashen waje.
A cewarsa za su duƙufa wajen farfaɗo da tattalin arzikin kasar da inganta rayuwar ƴan kasa a birni da karkara.
Ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.
(BBC Hausa)