Kusan awanni 24 bayan ya bar jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya zama jagoran jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP na ƙasa.
Takardar bayanan yanda ya zamanto jagoran an same ta ne a daren jiya Laraba, kuma ta baiyana cewa, Kwankwaso ya zama jagoran ne kwana ɗaya bayan ya fice daga PDP ya shiga NNPP a ranar Talata.
Haka kuma, an samar da Kwamitin Shugabannin Jam’iyyar na Ƙasa mai ɗauke da mutane 39 wanda mabiya Kwankwaso suka dafe manyan kujeru.
Yayinda masanin siyasa kuma tsohon Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Farfesa Rufai Alkali ya zama shugaban jam’iyyar NNPPn na ƙasa, yayinda kuma, aka baiyana AVM Ifemeje John Chris (mai ritaya) a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar.
Wanda ya zama Sakataren Jam’iyyar na ƙasa kuma shine, Dipo Olayoku; Sakataren Tsare-tsare kuma, Sanata Suleiman Hunkuyi, inda kuma Major Agbo ya zama Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar na Ƙasa.
Da yake jawabi a lokacin taron, Kwankwaso ya ce, ya ji daɗin goyon bayan da yake samu daga masoyansa da kuma magoya bayansa a jam’iyyar.
“Abinda ya rage mana shine, dukkaninmu mu koma tushe, jihohinmu da ƙananan hukumomi mu shigar da kanmu da ƴan’uwanmu kuma mu faɗawa ƴan Najeriya su shiga NNPP. Duk mun san cewa mutane sun gaji da jam’iyyun APC da PDP, hakan ce ma tasa a zaɓen da ya gabata aka sami ƙarancin fitowar mutane.
“Mun godewa Allah cewar mun samu sabuwar hanya domin samar da Najeriya mai inganci. Mutane sun gaji kuma suna son canji, NNPP ce kuma sabuwar hanyar da zata tabbatar da haka,” in ji Kwankwaso.
Ya kuma kushewa gwamnati mai ci wajen gaza magance matsalolin tsaro, inda ya koka kan harin da aka kaiwa jirgin ƙasa a ranar Litinin a Kaduna, abin da ya jawo mutuwar mutane da jin raunuka da kuma sace waɗansu.
(PUNCH)