
Kyaututtukan kudaden da kasashen da suka samu shiga gasar Kwallon Kafa ta Duniya ta 2022 wadda ake kammalawa yau a kasar Qatar sun kai dalar Amurka miliyan 440.
Gasar ta 2022 ta kasance tsakanin kasashe 32 daga sassan duniya gaba daya.
Kasashe 13 ne daga Europe, 5 daga Africa, 4 daga North America, 4 daga South America, da kuma ƙasashe 6 daga Asia.
Kasashen da suka fita a matakin group sune, Qatar, Ecuador, Wales, Iran, Mexico, Saudi Arabia, Denmark, Tunisia, Canada, Belgium, Germany, Costa Rica, Serbia, Cameroon, Ghana, Uruguay – kowannensu zai sami dala miliyan 9.
Kasashen da suka kai zagaye na biyu wato round of 16 sune USA, Senegal, Australia, Poland, Spain, Japan, Switzerland, South Korea – kowannensu zai sami dala miliyan 13.
Wadanda kuma suka kai matakin quarter- finals da suka hada da Brazil, Netherlands, Portugal, England – zasu sami dala miliyan 17 kowannensu.
Wadda ta zo na hudu, wato Morocco zata samu dala miliyan 25, yayin da Croatia da ta zo na uku zata samu dala miliyan 27.
Wadda zata zo na biyu kuma tsakanin Argentina da France zata samu dala miliyan 30, sai kuma wadda zata zo ta daya a gasar ta 2022 zata samu dala miliyan 42.
Gasar ta bana dai ta zo da karin kudi ga na daya da ya kai dala miliyan 40 sabanin yanda ta gabata a shekarar 2018.
A yau Lahadi 18 ga December, 2022 ne za a buga wasan karshe na gasar inda mai rike da kofi, France zata buga da kasar Argentina.