For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Labarai 10 Na Yaran Da Aka Taɓa Yi Wa Kisan Gilla A Najeriya

A shekarun baya-bayan nan za a iya cewa an samu ƙaruwar cin zarafin yara ta hanyar muzguna musu da wulaƙanta rayuwarsu da ma kashe su a Najeriya.

Duk da cewa babu wasu alƙaluma a hukumance da ke nuna yadda ƙaruwar ke hauhawa, amma abubuwan da suke faruwa a kewayenmu waɗanda kafafen yaɗa labarai ke ruwaitowa kawai sun isa a kafa hujja cewa yara na fuskantar munanan ƙalubale a wannan ƙarnin.

Kama daga yi musu fyaɗe da azabtar da su da yin safarar su da sacewa don neman kuɗin fansa da kuma sace su don sayar wa iyayen da ba sa haihuwa zuwa kashe su a wuraren da yaƙi da rikici ya yi ƙamari da kuma mayar da su ƴan gudun hijira ƙarfi da yaji.

Mafi munin abin da suke fuskanta kuma shi ne kisa, musamman ta hanyar yi musu kisan gilla.

A wasu yanayin kuma ko da sun tsira da ransu a irin harin da aka kai musu, to yaran kan dauwama cikin firgici sakamakon mummunan halin da aka saka su a ciki.

Waɗannan shekarun baya-bayan da ma waɗanda muke ciki yanzu, an samu yawaitar fyaɗe ga yara ƙanana, wasu ya yi sanadin kashe su, wasu kuma ya saka su a yanayi marar kyau.

Sannan babban abin tashin hankalin ma shi ne yadda makarantu, wuraren da ake ganin tudun mun tsira ne ga yara, a yanzu sun fara zama wuraren da iyaye ke zama cikin fargaba idan ƴaƴansu sun tafi.

KU KARANTA: Wanda Yai Garkuwa Da ‘Yar Shekara 5, Ya Kasheta Ya Daddatsa Gawarta

A Najeriya an ga yadda aka dinga kai hare-hare makarantu ana sace yara tare da yin garkuwa da su, ciki kuwa har da masu ƙananan shekaru.

A wasu lokutan kuma, wasu ɗaliban ne ke cin zarafin wasu ta hanyar zalintarsu, kamar yadda ya faru a wata makaranta a Maiduguri kwanan nan.

Mafi muni da sanya ɓacin rai kuma shi ne wanda malaman ne ma ke zama silar mutuwar wasu yaran ko yi musu wani mugun abu, duk da amincewar da iyaye suka yi na damƙa musu amanar ƴaƴansu, kamar dai yadda ake zargin wani malamin makaranta a Kano da sacewa tare da kashe ɗalibarsa Hanifa Abubakar mai shekara biyar.

Wannan maƙala ta yi waiwaye kan labarai na wasu yara 10 da suka taɓa fuskantar “kisan gilla” a sassan Najeriya, waɗanda kuma suka ta da hankalin ƴan ƙasar.

Wasu alƙaluma da asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya fitar sun nuna cewa shekarar 2021 an kai hari sau 25 a kan makarantu, an kashe yara 16 sannan an sace yara 1,440.

Mun zaɓi labarai na yara 10 ne saboda ba za mu iya kawo labaran dukkan yaran da suka taɓa fuskantar irin wannan lamari ba.

Kudanna nan domin karanta cikakken labarin a BBC Hausa

(BBC Hausa)

Comments
Loading...