Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalissar zartarwar Najeriya a yau Laraba, bayan bayyanar rashin Halartar Shugaba Buhari.
Ana raderadin cewa tun bayan dawowar Shugaban daga birnin New York na Amurka, har yanzu bai fito ba.
Wasu na ganin abin a matsayin killace kai saboda cudanyar da shugaban yai da jama’a a lokacin taron Majalissar Dinkin Duniya karo na 76.
