For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

LAFIYA: Alamun Farko Na Gane Barazanar Kamuwa Da Ciwon Bugun Zuciya

Gane alamun farko na kamuwa da ciwon bugun zuciya zai iya sa wa a ceci rai. Sai dai kuma alamun kamuwa da ciwon sun banbanta. Waɗansu mutanen suna samun ƙananun alamu ne, wasu kuma manyan alamu, wasu kuma ma babu wata alama da zata bayyana musu barazanar.

Bugun zuciya na faruwa ne lokacin da jijiyar da ke kai jini da iskar oxygen cikin zuciya ta toshe. Wasu lokutan a kan samu gudajin jini saboda wasu dalilai, waɗanda sune ke toshe jijiyar.

KARANTA WANNAN: Mutane 83 Sun Mutu, 836 Sun Kamu Yayinda Cutar Diphtheria Ta Yaɗu A Jihohi 8 Na Najeriya

Tsohon Darakta kuma Shugaban Sashin Kula da Cututtukan da ba sa Yaɗuwa a Ma’aikatar Lafiya, Dr. Nnenna Ezeigwe ya ce, huɗu cikin biyar na mutuwar da ake ta dalilin matsalar zuciya na faruwa ne saboda bugun zuciya ko mutuwar ɓarin jiki.

Ga wasu daga alamun cewar mutum na fuskantar barazanar samun bugun zuciya:

  1. Ciwon ƙirji
  2. Sarƙewar nunfashi
  3. Yawan yin gumi
  4. Jin ciwon jiki a kafaɗu, hannaye, baya, wuya, muƙamuƙi da saman ciki
  5. Jin alamun kamuwa da rashin lafiya

Masana sun ce, wasu bugun zuciyar suna faruwa ne kai tsaye bagatatan, amma mafi yawan mutane suna samun jin alamu na awanni, kwanaki, ko makonni kafin zuciyar ta su ta buga.

Abu mafi wayewa ga kowa shine, duk lokacin da mutum ya ji waɗancan alamu, ya garzaya asibiti wajen likita domin a tabbatar masa sannan a ɗora shi a kan magani da shawarwari.

Comments
Loading...