Wani mutum da ba a tantance ba wanda yai kokarin satar wayar transfoma yam utu a dalilin jan da wuta tai masa a safiyar Alhamis din nan a Unguwar Labour ta yankin Tumfure a karamar hukumar Akko ta jihar Gombe.
Dr. Adakole Elijah, shine shugaban sashin kasuwanci na Jos Electricity Distribution Company (JEDC), ya tabbatar da lamarin ga kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN yau Alhamis a Gombe.
KU KARANTA WADANNAN:
- ‘Yansanda Sun Kama Sojan-Gona Na Cutar Masu A Daidaita Sahu A Kano
- Wani Dan Bindiga Ne Ke Iko Da Kasarmu Ba Gwamnati Ba – Kungiyar Gobirawa
- Fursunoni Sama Da 3000 Ne Suka Gudu A Najeriya – Ministan Cikin Gida
Dr. Adakole ya ce, “a 16 ga Disamba, da misalin 3:30 na asuba, wuta ta ja wani mai satar wayar lantarki kuma ta kasha shi yayin da yake kokarin yin sata a transfoma mai lamba 1 a Tumfure mai karfin 11kv.”
Ya kara da cewa an sanar da lamarin ga ofishin ‘yansanda na Tumfure, in da nan take ‘yansanda suka sakko da marigayin wanda ba a iya ganewa ba.
Ya kuma yi kira ga ‘yan unguwa da ko da yaushe su zama masu kula da kuma sanar da duk wanda sukai zargin zai lalata musu wutar lantarkinsu.
Yayinda kuma yai kira ga masu mummunan halin satar kayan lantarkin da su yi duba ga irin matsalar da al’umma, JEDC da su kansu ke shiga dalilin hakan.