Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa a Najeriya, NARD, ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
Shugaban NARD na ƙasa, Innocent Orji ne ya bayyana hakan a saƙon da ya aike a jiya Talata da daddare.
Ya bayyana cewa, manyan buƙatun likitocin sune gaggauta biyan kuɗin neman ƙwarewa na 2023 wato 2023 Medical Residency Training Fund (MRTF), da kuma gaggauta sakin takardar bayanan yanda za a biya a kuma maye gurbin kuɗaɗen da suke bi.
Sauran sune, sake duba tsarin albashin likitoci na CONMESS tare da dawo da cikakken albashin kan tsarin da yake a shekarar 2014, da kuma biyan bashin albashin albashi da ya samo asali daga ƙarin mafi ƙarancin albashi ga likitocin da ba su samu ba.
Wani Labarin: CIRE TALLAFI: Ma’aikata Zasu Tsunduma Yajin Aiki Ranar Laraba Mai Zuwa A Najeriya
Likitocin kuma suna buƙatar a janye matakin rage darajar da aka yi wa tsarin rijistar zama ɗan ƙungiyar likitoci ta Medical and Dental Council of Nigeria (MDCN).
Da ma a sanarwar da ta fitar ranar 5 ga watan Yuli, ƙungiyar NARD ta baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin sati biyu domin ta biya mata buƙatunta ko kuma ta fuskanci yajin aikin sai baba ta gani.
Likitocin masu neman ƙwarewa sun gudanar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki 5 wanda suka fara ranar 17 ga watan Mayu, da nufin tursasa gwamnati ta biya musu buƙatunsu kafin ranar rantsuwa ta 29 ga watan Mayu suka kuma janye a ranar 21 ga watan ba tare da buƙatun nasu sun biya ba.
A ranar Litinin da ta gabata, Kakakin Majalissar Wakilai, Tajuddeen Abbas ya buƙaci likitocin da su janye yunƙurinsu na tsunduma yajin aikin a lokacin da ake tattaunawa tsakanin shugabancin majalissa da na ƙungiyar NARD a Abuja.
(NAN)
