For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Likitocin Asibitin FMC Owo Sun Shiga Yajin Aiki Saboda Wahala

Mambobin Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa na asibiti Federal Medical Center da ke garin Owo a Jihar Ondo sun fara yajin aikin gargadi na sati biyu saboda wahalar da ma’aikata ke sha a asibitin.

An rawaito cewa, likitocin sun dakatar da duk wata hada-hadar aiki a asibitin bayan kungiyar ta yi zama da mambobinta a jiya.

Shugaban kungiyar, Dr. Olaopa Gideon ya ce, daukar matakin shiga yajin aikin wani abu ne na dole saboda suna aiki ne cikin mawuyacin hali.

Ya bayyana cewa, likitoci masu neman kwarewa da sauran ma’aikatan lafiya 80 ne kacal a asibitin, haka kuma tun shekarar 2018 ba a dauki ko mutum daya aiki a asibitin ba.

Ya kara da cewa, a yanzu haka, a asibitin, mutum daya yana aikin mutane 5 ne tun shekarar bara, kuma ma’aikata da dama na barin asibitin.

Haka kuma, Dr. Gideon ya ce hukumar asibitin ba ta biyansu kudin karin aikin da suke yi yayin da kullum suke cikin aiki dare da rana.

Cikin takardar bayan taron da kungiyar ta fitar, ta sanya matsalar rashin kyakkyawan muhalli ga yan’uwansu da ke aiki a reshen asibitin na garin Akure.

Comments
Loading...