For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Likitocin FMC Birnin Kudu Sun Nuna Goyon Baya Ga Dr Usman Sanusi Usman

Daga: Kabiru Zubairu

Kungiyar Ma’aikatan Lafiya (Nigerian Medical Association (NMA) reshen asibitin Federal Medical Center, Birnin Kudu ta bayyana bukatar samun kwararre kuma wanda ya san matsalolin asibitin domin jagorantar asibitin.

Kungiyar ta bayyana hakanne a takardar bayan taron da Dr. Hayatu Gwarzo da kuma Dr. Mohd Riyad suka sanyawa hannu kuma JAKADIYA ta samu a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce “Duba da duk tsarar asibitin, FMC Birnin Kudu shine mafi ci baya a bangaren ma’aikata da gine-gine da kayan aiki, saboda gazawar jagororin da suka gabata wajen fahimtar matsalar da ke addabar asibitin.”

“Akwai tsananin bukatar samun habbaka gine-gine da kayan aiki, haka kuma akwai bukatar samar da cigaba a kayan aikin da ake da su da kuma samar da walwala ga ma’aikata”

Kungiyar ta ce duba da yanayin da asibitin ke ciki na bukatar ci gaba, akwai bukatar samun wanda ya san matsalolin kuma yake da himma da fatan kawo cigaba da magance daddun matsalolin asibitin.

Sanarwar ta kuma ce “tun da akwai daya daga cikinmu wanda aka zaba kuma aka bayyana sunansa, mun amince mu bi shi ya jagorance mu domin yin abin da ya dace.

“Wannan kuwa ba kowa ba ne sai Dr. Usman Sanusi Usman, kwararren likita a fannin lafiyar al’umma kuma kwararre a sanin shugabanci, kuma ya yi aiki a fannoni da dama na ciyar da bangaren lafiya a asibitin da ma matakin jiha.”

A yanzu dai batun shugabancin asibitin na gaban gwamnatin tarayya inda ake dakon hukuncinta wajen nada sabon shugaba, bayan karewar wa’adin tsohon shugaban asibitin, Farfesa Suleiman Idris Hadejia, a farkon watan Satumba.

Comments
Loading...