Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB, ta sanar da ranakun fara rijistar jarabawar a shekarar 2023, inda ta ce za a yi rijistar a tsakanin Asabar, 14 ga watan Janairu zuwa Talata, 14 ga watan Fabarairu, 2023.
Hukumar ta sanar da hakan ne a jiya Talata a wata sanarwa da Shugaban Sashin Yada Labarai na Hukumar, Fabian Benjamin ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta ce, hukumar shirya jarabawar ta fitar da ranakun da zata gudanar da manyan aiyukanta na shekarar 2023 ne a karshen zaman tattaunawar shugabanninta wanda ta yi a Abuja.
Sanarwar ta ce ranakun da aka bayyana a sama ba su shafi masu rijistar DE ba, inda shi DE za a yi rijistarsa daga ranar Litinin, 20 ga watan Fabarairu zuwa Alhamis 20 ga watan Afirilu, 2023.
Hukumar ta kuma sanya ranar Alhamis, 16 ga watan Maris, 2023 a matsayin ranar jarabawar gwaji ga ‘yan JAMB.
Haka kuma, hukumar, bayan duba yanayin aiyukanta, ta sanya Asabar, 29 ga watan Afirilu zuwa ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, 2023 a matsayin ranakun rubuta jarabawar JAMB.