For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ma’aikata Sun Rufe Filin Jirgin Sama Na Legas

An soke tashin jiragen da aka shirya tashinsu yau da safe a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas, sakamakon zanga-zangar ma’aikatan filayen jiragen sama.

Lamarin ya sanya fasinjojin da suka yi sammako domin yin tafiye-tafiye cikin halin kunci.

Su dai ma’aikatan filayen jiragen sama na zanga-zangar ne saboda korar wasu daga cikin mambobin kungiyarsu 34 daga aiki, da kamfanin Bi-Courtney Aviation Services Limited (BASL) ya yi.

Kungiyar ma’aikatan sun yi zargin korar wasu daga cikin ma’aikatan nata da kamfanin ya yi ba ya bisa tsarin doka.

A wata sanarwa da kamfanin jirgin sama na Ibom Air, ya aikewa fasinjojinsa ya ce wannan zanga-zanga ta shafi zirga-zirgasa na yau a ciki da wajen Legas.

BBC Hausa

Comments
Loading...