For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ma’aikatan Bogi Na Jawowa Jigawa Asarar Naira Biliyan 2.5 Duk Wata

Gwamnatin jihar Jigawa na asarar Naira Biliyan 2.5 a duk wata ga ma’aikatan bogi a bangaren ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi.

Wannan na kunshe ne a cikin rahoton kwamitin tantance ma’aikata na jihar karkashin jagorancin dan majalisar jiha Surajo Kantoga, mai wakiltar mazabar Birnin Kudu a majalisar dokokin jihar.

Da yake gabatar da rahoton kwamitin ga Shugaban Kungiyar Shugabannin Kananan Hukumomi (ALGON) ta jihar, Bala Usman Chamo a ranar Juma’a, dan majalissar ya ce jihar na asarar sama da Naira Biliyan 2.5 duk wata wajen biyan ma’aikatan bogi a matakin jiha da na kananan hukumomi.

Kantoga ya ce ma’aikatun da abin ya shafa bangaren malamai ne da ma’aikatan kananan hukumomi a fadin duk kananan hukumomi 27 na jihar.

Haka kuma, kwamitin ya ce, yayin aikin sa ya gano cewa akwai kimanin ma’aikatan bogi 84 da kimanin malamai 41 da ba su da kwarewa da kuma cancantar koyarwa bangaren ilimi.

“Kwamitin ya kuma gano cewa an ciyar da malamai 29 gaba ba bisa ka’ida ba yayin da aka dauki wasu aiki kwanan nan suma ba bisa ka’ida ba.

Shugaban ALGON na jihar, Bala Usman Chamo, yayin karbar rahoton kwamitin ya yabawa shugaban kwamitin da mambobin sa.

Ya kuma ba da tabbacin aiwatar da rahoton sakamakon binciken kwamitin yadda ya kamata don tabbatar da kwanciyar hankali, gaskiya da adalci a tsakanin ma’aikatan gwamnatin jihar.

Comments
Loading...