For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Mafi Yawan Shugabannin Najeriya Suna Da Ƙarancin Sanin Mene Ne Ci Gaba – Obasanjo

A ranar Litinin da ta gabata, tsohon Shugaban Ƙasa, Obasanjo ya kushe shugabannin Najeriya inda ya ce, mafi yawansu ba su da komai a kansu game da al’amuran samar da ci gaban al’umma.

Obasanjo ya yi wannan magana ne a Abuja lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen ƙaddamar da littafi mai suna, ‘Reclaiming the Jewel of Africa (Ƙwato Darajar Afirka),’ wanda tsohon Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Sdanya Hannu Jari wanda kuma ya riƙe Ma’aikatar Kuɗi, Olusegun Aganga.

Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Tinubu Shawara kan Harkokin Kuɗaɗe, Olawale Edun ne ya ƙaddamar da littafin.

Taron ya samu halartar da dama daga cikin tsofi da kuma masu riƙe da madafun iko a Najeriya, yayin da tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan da Obasanjo suka halarta ta yanar gizo.

Obasanjo ya bayyana cewa, kamata yai a mai da hankali kan shugabanci, domin shine mafi muhimmanci wajen samarwa da kuma daidaita ci gaban al’umma, musamman a ƙasa irin Najeriya.

Obasanjo ya ce, inda za a tambayi mafi yawan masu neman mulki dalilin da yasa suke nema, za a tausayawa ƙasarmu saboda irin jahilcin da suke da shi game da samar da ci gaba.

Obasanjo ya ce, domin samun zaman lafiya, tsaro, nutsuwa, hangen nesa, ci gaba, da samun bunƙasuwa dole ne a gwama waɗannan abubuwa a lokaci guda.

Ya ƙara da cewa, duk shugaban da ya gaza gane waɗannan sannan ya gaza haɗa su a waje guda domin samarwa a gwamnati to babu abin da zai iya na a zo a gani.

Obasanjo ya kuma ce, ɗorawa a kan tsare-tsare da kuma tsayuwa a kai wani abu ne da shugabanci yake buƙata domin samun nasara.

Ya ce, Najeriya ba ta ƙamfar tsare-tsare, sai dai samun abin da ya dace wajen gudanar da tsare-tsaren ne ya ci gaba da zama matsala.

Tsohon Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa, idan aka gyara matsalar shugabanci a ɓangaren halayya, ɗabi’u, al’adu, fahimata, ƙoƙari da soyayyar ɗan’adam haɗi da tsoron Allah, komai zai samu a Najeriya da ya shafi ci gaba, Najeriya zata zama gagarumar ƙasa a duniya.

Ya kuma ce, cikin shekaru 63 da Najeriya ta kasance da ƴancin kanta, ba ta yi abin da akai zato ba, ta kunyata kanta, ta kunyata Afirka, ta kunyata baƙar fata, ta kuma kunyata duniya.

Comments
Loading...