
Magoya bayan Moroko sun shirya tsaf domin nuna farin ciki da wasan neman na uku da kasarsu za ta yi da Croatia a wasa na biyun karshe a gasar cin kofin duniya.
Moroko ce kasar Afrika ta farko kuma ta Larabawa da ta fara zuwa wasan kusa da na karshe a duniya, amma ta yi rashin sa’a a wasan a hannun Faransa mai rike da kofin.
Birnin Casablanca ya yi tsit tun bayan rashin nasarar da kasar ta yi a hannun Faransa a ranar Laraba.
Magoya bayan sun ce ba su ji dadain sakamakon wasan ba, amma suna jin cewa suna alfahari da kasarsu.
Mutane da dama dai suna tsammanin ba za a ga magoya bayan ba da yawa, saboda rashin da nasarar da ta yi a baya.
BBC Hausa