Gwamna Mai Mala Buni ya amince da hawan babura (mashin) mai kafa biyu a yankunan Yobe zone B da zone C bayan dawowar zaman lafiya a jahar Yobe.
Gwamnan ya sanar da hakan ne yanzu, a fadar Sarkin Nguru.
KU KARANTA: An Gano Gawarwakin Mutane Fiye Da 140 Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Zamfara
Kafin hakan dai a lokacin yakin neman zabensa a ranar 17 ga watan Maris na 2019, Buni yayi alƙawarin cewa idan aka zaɓe sa zai amince a dawo da hawan Babura a jihar.
Yobe zone B sune kananan hukumomin Potiskum, Fune, Nangere, da kuma Fika. Zone C kuma sune Gashua, Jakusko, Machina, Yusufari, Nguru , da kuma Karasuwa.
Daga: Muhammad Sulaiman Yobe