Tsohon Mai Taimakawa Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar a kan Harkokin Kafafen Yaɗa Labarai, Bello Zaki, ya fice daga jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar NNPP.
Tsohon Mai Magana da yawun Badarun, ya sanar da komawarsa jam’iyyar NNPP ne jiya Litinin a yayin zaɓen shugabannin jam’iyyar na jiha wanda aka gudanar a Dutse.
Bello Zaki ya ce, ya shiga jam’iyyar NNPP ne tare da magoya bayansa saboda gazawar jam’iyyar APC na samar da ingantaccen shugabanci ga ƴan Najeriya.
Da yake jawabi a wajen taron zaɓen shugabannin, shugaban kwamitin shirya zaɓen da uwar jam’iyyar NNPP ta turo daga Abuja, Mr Takwak Mikaial ya ce, an samar da jam’iyyar ne a kan tsarin demokaraɗiyya.
Ya ƙara da cewa, sabbin shugabannin jam’iyyar na jihar, an samar da su ne ta hanyar maslaha.
Ya kuma baiyana cincirindon taron jama’a a wajen zaɓen shugabannin a matsayin alamar ƙwarin guiwa da kyakkyawan zato da mutanen Jigawa ke da su game da jam’iyyar NNPP.
(DAILY POST)