For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalisar Amurka ta Amince Da Kara Yawan Bashin Da Kasar Ke Ciyowa

Majalisar dokokin Amurka ta bai wa gwamnatin kasar dama ta dan lokaci domin ƙara yawan bashin da a ƙa’ida ya kamata ta ciwo, wanda ƙwararru ke cewa yin hakan zai kawar da wata gagarumar matsala ta tattalin arziki da ƙasar ba ta taba shiga irinsa a tarihi ba.

BBC Hausa ta rawaito cewa, dukkan ‘yan jam’iyyar Democrats 50 sun kaɗa ƙuri’ar amincewa, yayin da 40 na jam’iyyar Republican suka ƙi amincewa, sai kuma biyu da ba su kada ƙuri’ar ba.

Wakiliyar BBC ta ce dole sai ‘yan majalisar wakilai sun amince da dokar kafin Shugaba Joe Biden ya rattaba mata hannu.

Dokar da Biden zai sanyawa hannu za ta kara adadin kudin da za a ciwo a matsayin bashi da dala biliyan 480, domin cike giɓin kudaden da za a kashe zuwa 3 ga watan Disamba mai zuwa.

Comments
Loading...