Biyo bayan yadda ake cigaba da kiraye-kirayen tura sakamakon zabe ta fasahar sadarwar, majalisar dattawa a yau Talata tayi alkawarin bawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC damar gudanar da zaben yadda take so.
Wannan na zuwa ne, bayan majalisar ta sake yin Nazari kan matsayarta na bawa INEC damar tura sakamakon zabe ta yanar gizo, karkashin kulawar hukumar Sadarwa ta Kasa wato NCC da sahalewar Majalisar Kasa.
Karkashin sashe na 52 (2) na kundin sake tsarin zabe, majalisar ta amince a tura sakamakon zaben kamar yadda hukumar INEC ta bukata ciki harda ta cikin fasahar sadarwa.
Hakan na daga cikin shawarwarin da majalisar dattawa ta dauka, a lokacin da take amincewa da kudurin, kamar yadda majalisar wakilai da dattawa suka amince a baya.
Da yake gabatar da kudurin kawo sauye-sauyen a zaman majalisar dattawan shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Yahaya Abdullahi, ya ce bayan dogon nazarin kan rahoton da kwamatin hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa wato INEC ya gabatar , an yi Nazari kan wasu batutuwa wanda suke bukatar matakai, batutuwan da suke bukatar matakan sun hada da sashe na 43,52,62,87.
Sashe na 87 yana Magana kan matakan da ake bukata jam’iyun siyasa su dauka a lokacin tantance yan takarkaru.
Majalisar dattawa tun da farko, ta amince da kudurin jam’iyu su gudanar da zaben cikin gida ta fannin kato bayan kato ko kuma ta fannin tura Deliget.
Sanata Adamu Allero, na daga cikin wadanda suka goyi bayan jam’iyu su rika yin zaben cikin gida ta hanyar kato bayan kato, saboda a nasa ra’ayin hakan zai sake karfafa demokradiya, inda ya kara da cewa hakan zai rage yawan amfani da kudade a lokacin yin zabukan cikin gida.
Sai dai a rahoton da Kwamatin hukumar INEC ya gabatar ya bayyana cewa majalisar tana da zabi kan hanyoyin da za’a gudanar da zaben cikin gida ga jam’iyu, inda wasu yan majalisar suka amince da zaben kato bayan kato wasu kuma basu amince da hakan ba.
To sai dai Sanata Smart Adeyemi, bai amince da kudurin Sanata Adamu Allero ba, inda ya bayyana cewa shi yafi goyan bayan zabukan cikin gida ta hanyar yin wakilan da jam’iya.
A cewarsa, zabukan cikin gida ga jam’iyu ta hanyar tura wakilai shine mafi ma’ana, saboda mafiya wayan masu zaben yan takarkarun basu da ilimi, kuma suna bukatar fadakarwa, matukar ana bukatar su fito suyi zabe, inda ya kara da cewa yin zabe da Dalaget shine abu mafi sauki.
Bayan an fafata a zaman majalisar ne, mafiya yawan yan majalisar sun goyi bayan yin zabe kato bayan kato, kuma majalisar dattawa ta amince da hakan.