For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalisar Dattawa Ta Ki Amincewa Da Kasafin Kudin 2023

Majsalair Dattawa ta ƙi amince wa da kasafin kudin shekarar 2023 da ta shirya amince wa da shi a ya yin zaman majalisar na yau Alhamis.

Shugaban Majalisar Dattawan, Ahmad Lawan ya ce, rashin amincewa da kasafin kuɗin ya biyo bayan kurakuran da kasafin kudin ke kunshe da su, daga banagren gwamnati.

“Sakamakon wasu ƙalubale, ba za mu iya karbar rahotan kwamitin kula da kasafin kudin ƙasa ba, saboda ya zo majalisa da matsaloli.

Ahamd Lawan ya ce sai a jiya majalisar dattawan suka kuma karɓar ƙarin wasu buƙatu daga Shugaban Kasa na kari a kasafin kudin na wasu ayyuka na musamman na naira tiriliyan 23.7.

Ya ce ranar Laraba, 28 ga Disambar da muke ciki suka sake tsayarwa domin amincewa da kasafin.

Comments
Loading...