For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissar Dattawa Ta Gabatar Da Kudirin Hana Karbar Kudin Haya Na Tsawon Shekara Sai Dai Wata-Wata

An karanta kudirin doka da yake neman a mayar da neman kudin hayar gida, shago, office sama da na watanni uku haramun a Majalissar Dattawa yau Talata.

Dan Majalissar Dattawa daga jihar Kogi, Mazabar Majalissar Dattawa ta Kogi ta Yamma, Samart Adeyemi ne ya gabatar da kudirin mai taken ‘Dokar Biyan Kudin Hayar Gidaje, Ofisoshi da Sauransu ta 2022.

Sanata Adeyemi wanda yaiwa ‘yan jarida bayani jim kadan bayan kudirin ya tsallake karatu na daya, ya ce kudirin zai bayar da dama ga masu shiga haya su biya kudin hayar da bai haura na watanni uku ba a farko, daga baya kuma yana biyan wata-wata.

KU KARANTA: FMC Birnin Kudu Zai Kulla Alakar Aiki Da FUD

Ya ce “mun gano cewa, masu gidajen haya suna takurawa masu shiga haya da su biya kudin shekara ko shekara biyu kafin a ba su makullin shiga gidajen. Wannan zai iya zama ba damuwar kowa ba ce, amma wajensu wannan ba karamin cin tuwo yake musu a kwarya ba. Da yawan ‘yan Najeriya suna bukatar dokar da za ta ba su damar biyan bukatunsu cikin sauki bayan sun biya kudin haya.

“Da yawan masu gidajen haya, ba bashi suka karba ba wajen gina gidajensu; suna samun ribarsu ne kawai daga tsarin. Sannan kuma suna mayar da rayuwa mai wahala ga talakawan Najeriya wadanda ba su da damar yin irin yanda suke su samar da gidajen.

“Ana gina gidaje da yanayin da, talakan Najeriya ba zai iya shiga ba. Da yawa suna shiga harkar da ba ta dace ba wajen hada kudin hayarsu, yayin da mata ke fadawa karuwanci a kan hakan.

“Dokar da muka gabatar, ta ware biyan kudin haya na watanni uku. Sannan bayan karewar watanni ukun, masu zaman hayar za su na biya wata-wata.

“Akwai masu zaman hayar da albashinsu yana gogayya da kudin hayarsu, saboda suna zaune a birane kamar Abuja. Dokar za ta kare ma’aikata talakawa daga dukkan kalar cin zarafi.”

Comments
Loading...