For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissar Dattawa Ta Tabbatar Da Mutane Bakwai A Matsayin Kwamishinonin INEC

Majalissar Dattawa ta tabbatar da mutane bakwai wadanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika mata a matsayin Kwamishinonin Zabe na Kasa da kuma Kwamishinan Zabe na jiha na Hukumar INEC.

Tabbatarwar da majalissar tai a yau Laraba, ta samo asali ne daga rahoton kwamitin INEC na majalissar.

Wadanda aka tabbatar din sun hada da Malam Mohammed Haruna (dan jihar Niger) a matsayin Kwamishina na Kasa; Mrs May Agbamuche-Mbu (dan jihar Delta) a matsayin Kwamishina na Kasa; Ukeagu Kenneth Nnamdi (dan jihar Abia) a matsayin Kwamishina na Kasa; da Major General A.B. Alkali Mai Ritaya (dan jihar Adamawa) a matsayin Kwamishinan Kasa.

Sauran sun hada da Prof. Rhoda H. Gumus (dan jihar Bayelsa) a matsayin Kwamishina na Kasa; Mr. Sam Olumekun (dan jihar Ondo) a matsayin Kwamishinan Kasa; da kuma Olaniyi Olaleye Ijalaye (dan jihar Ondo) a matsayin Kwamishinan Jiha.

Shugaban Kwamitin INEC na Majalissar Dattawa, Sanata Kabiru Gaya, a gabatar da jawabinsa, ya bayyana cewar bukatar Shugaba Buhari ta samo asali ne daga Sashi na 153(1)(f) da kuma Sashi na 154(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 wanda akaiwa gyara.

Comments
Loading...