Shugaban Kwamitin Kudi na Majalissar Dattawa, Sanata Olamilekan Adeola, a jiya Laraba ya bayyana cewa sama da ma’aikatu 400 ne daga cikin ma’aikatu 541 na Gwamnatin Tarayya za a soke a shekarar 2023.
Wannan aiki dai ya samo asali ne daga shawarar da Kwamitin Shugaban Kasa kan Inganta Ma’aikatu karkashin shugabancin Stephen Orosanye, inda kwamitin ya bayar da shawarar barin iya ma’aikatu 106.
Ya bayyana cewa, samar da kudaden shiga shine abu mafi muhimmanci wanda Gwamnatin Tarayya za tai la’akari da shi kafin ci gaba da kasancewa da ma’aikatu 106 ko soke ma’aikatu 400.
Sanatan mai wakiltar Lagos ta Yamma, ya bayyana cewa, “Muna goyon bayan aiwatar da rahoton Orosanye domin magance zubar jinin tattalin arziki.”