For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissar Dinkin Duniya Na Zargin Rasha Da Zagon Kasa

Jami’an diflomasiyya sun zargi Rasha da dakile ayyukan kwamitocinsu da ke sanya ido kan biyayya ga takunkuman haramta cinikin makamai da na tattalin arziki da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa wasu yankunan da kasashe masu fama da rikici ciki har da Mali.

Jami’an Diflomasiyyar kwamitocin na Majalisar, sun ce yankunan da aka kakabawa takunkumai saboda dalilai daban-daban na samun goyon bayan Rasha ta karkashin kasa, lamarin da Majalisar ta bayyana da yunkurin zagon kasa ga aiyukanta.

Ikirarin Majalisar na zuwa ne a dai-dai lokacin da Rashan ke ci gaba da yunkurin fadada ayyukan ta a kasashen Afirka ciki har da kasashe renon Faransa, da yankunan da har ya zuwa yanzu su ke karkashin ikon kasar da tai musu mulkin mallakar.

Majalisar Dikin Duniya ta kuma zargi Rashan da kin bayar da hadin kan da ya kamata cikin kwamitocinta a aiyukan da suka shafi zaman lafiyar Duniya da kuma dakile yunkurin tayar da zaune tsaye.

A cewar Majalisar ta bakin jami’an Diflomasiyyar, kwamitocin Rasha na jan kafa wajen taimakawa tabbatar da takunkumin da aka sanyawa Jamhuriyar Africa ta tsakiya da kuma Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, har ma wa’adin da aka dibar musu ya kare.

Majalisar ta gwada misali da yadda wa’adin takunkumin da aka sanyawa kasashen Sudan da Mali ya kare, ba kuma tare da Rashan ta bayar da hadin kan da ya kamata ba wajen zaman tattaunawa kan batun.

Comments
Loading...