Majalissar Jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar da ta gina reshen makarantar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (Kano State Polytechnic) a karamar hukumar Rogo da ke jihar.
Wannan ya biyo bayan kudirin da dan majalissar jihar mai wakiltar Rogo, Dahiru Zarewa.
Zarewa ya bayyana cewa, samar da reshen makarantar zai temaka wajen bunkasa tattalin arziki da kuma rage matsalar rashin aikin yi ta hanyar koyar da sana’o’i.
‘Yan majalissa masu wakiltar Sumaila, Dala, Kiru da Tudun Wada sun baiyana cewa, kasancewar jihar Kano mai yawan jama’a tana bukatar karin makarantu domin bayar da dama ga matasa.