For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissar Tarayya Na Neman A Baiwa Sarakunan Gargajiya Aiki A Kundin Tsarin Mulki

Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan ya baiyana cewa za a gabatar da kudiri a Majalissar Tarayya domin sarakuna su samu aikin yi a Kundin Tsarin Mulki.

Ahmad Lawan, wanda yai maganar a yau Asabar a fadar Sarkin Ilorin, Mai Martaba Alhaji Ibrahim Sulu Gambari, a lokacin da ya kai masa ziyara, ya ce, wannan zai zama wani bangare na gyaran kundin tsarin mulkin kasa da ake kokarin yi.

Ya je Kwara ne domin ya halarci taron kaddamar da shirin tallafawa masu sana’o’i na shekarar 2022 wanda sanata mai wakiltar Kwara ta Arewa, Sadiq Sulieman Umar zai yi.

Mai baiwa Shugaban Majalissar Dattawa Shawara kan Kafafen Yada Labarai, Ola Awoniyi ne ya sanar da hakan ga ‘yan jarida a takarda mai taken: “Zamu Mika Bukatar Samar da Aikin Sarakuna a Kundin Tsarin Mulki – Shugaban Majalissar Dattawa.”

Takardar ta ce, “A majalissa ta 9, mun amince cewa, iyayen mu sarakuna ya zama dole su zama suna da baiyanannen aiki da kuma gudunmawar da za su bayar a kundin tsarin mulkin mu, saboda haka mu samu damar samun tsarin gamammiyar gwamnati da zai tabbatar da cewa sarakuna suna yin abubuwan da suke yi yanzu haka bisa kan tsarin gwamnati.”

A zuwan sa fadar Ilorin, Ahmad Lawan ya samu rakiyar Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq da sauran sanatoci shida, da suka hada da Aliyu Sabi Abdullahi(Mataimakin Bulaliyar Majalissar Dattawa), Bello Mandiya, Yakubu Oseni, Ibrahim Oloriegbe, Lola Ashiru da kuma Smart Adeyemi. (PUNCH)

Comments
Loading...