A kokarin Majalissar Tarayyar Najeriya na gyaran Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999, Majalissar ta amince da damar fitowa takarar kujerar shugabanci ba tare da amfani da jam’iyya ba – abin da ake kira da indifenda.
Majalissar dai ta yi hakan ne a jiya, lokacin da take amincewa da kudirorin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999, inda ‘yan Majalissar guda 267 suka amince da kudirin takarar indifenda.
Dan takarar indifenda dai shine wanda zai fito takarar neman Shugabancin Kasa, Gwamna, Dan Majalissar Wakilai, Dan Majalissar Dattawa, Dan Majalissar Jiha, Shugaban Karamar Hukuma, ko Kansila ba tare da amfani da jam’iyya ba.
TASKAR YANCI ta gano cewa, da yawan mutane na kyautata zaton cewa, hakan zai magance matsalar danniya da jam’iyyu ke yi da kuma matsalar ubangida a siyasar Najeriya.
Yanzu dai abun jira a gani shine ko kudirin zai samu tsallakewa a matakin majalissun jihohi.