For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissar Tarayya Za Tai Gyare-Gyare 55 A Kundin Tsarin Mulkin 1999

Majalissar Tarayya na duba gyare-gyare 55 da za tai a kundin tsarin mulkin shekarar 1999 inji Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege.

Da yake jawabi a taron kwanaki biyu na kwamitocin gyaran kundin tsarin mulki na majalissun biyu, Majalissar Dattawa da Majalissar Wakilai, Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawan ya ce, gyare-gyare 55 da ake nazari a kai, sun samo asali ne daga ra’ayoyin da jama’ar Najeriya suka gabatar ga Majalissar Dattawa da ta Wakilai.

Ya ce kwararru sun tantance gudunmawar da aka samu, haka suma Majalissar Dattawa da ta Wakilai, inda aka tabbatar da wasu daga ciki tare da zubar da wasu da kuma kawo wasu sabbi.

Ya ce tsarin gudanar da aiyukan kwamitocin gyaran kundin tsarin mulkin ya samu tsaiko dalilin annobar Korona, inda ya kara da cewa, duk da haka ‘yan majalissun suna kokari domin sauke nauyin da aka dora musu.

Ya yabawa mambobin kwamitocin bisa nasarar da aka cimma kawo wannan lokaci, inda ya kuma ce, aikin tantance gudunmawar da aka samu ba karamin aiki ba ne.

Ya yi kira domin a samu cikakken hadin kan mambobin kwamitocin domin tabbatar da samun nasarar tattarawa da kuma hada rahotannin da aka samar a kowacce majalissa.

Shima a nasa bangaren, Mataimakin Kakakin Majalissar Wakilai, Idris Wase ya yi kira ga samun hadin kan mambobin domin tabbatar da an mika kudire-kudiren ga majalissun jihohi kafin karshen watan Fabarairun da muke ciki.

Babban Daraktan Cibiyar Wayar da Kai Kan Tsare-tsaren Majalissa (Policy Legislative Advocacy Centre (PLAC), Clement Nwankwo ya ce, wasu daga cikin bangarorin da akaiwa gyara sun hada da bangaren inganta tsarin kananan hukumomi, inganta tsarin bangaren shari’a, da kuma gurabe na musamman ga mata a majalissun dokoki na tarayya da kuma jihohi da ma sauran batutuwa.

Majalissar Tarayyar za ta rarraba kudire-kudiren gyaran kundin tsarin mulkin domin magance yanayin da zai sa a yi watsi da kudire-kudiren gaba daya a lokacin da Shugaban Kasa ya ki sanya masa hannu. (THE NATION)

Comments
Loading...