For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissar Wakilai Ta 10 Ta Saki Ƙudireƙudirenta 6

Majalissar Wakilai ta 10 ta saki ƙudireƙudirenta shida da take son ta cimma a cikin shekaru huɗun da take da su domin samun nasara da kuma shigar da kowa a faɗin ƙasa.

Ɗan Majalissa, Julius Ihonvbere wanda shine Shugaban Masu Rinjaye a Majalissar kuma Shugaban Kwamitin Wucin Gadi kan Tsare-tsaren Majalissa ne ya sanar da haka yau Litinin a Abuja.

Ya bayyana ƙudireƙudiren da cewar sune, bunƙasa tattalin arziƙi da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗe, samar da ababen more rayuwa, ilimi da bunƙasa rayuwar ɗan’adam.

Sauran sune, samar da kulawar lafiya ga kowa, yin buɗaɗɗiyar gwamnati, yin gaskiya, da kuma samar da tsaro ga mutane da dukiyoyinsu.

Ihonvbere ya ce ƙudireƙudiren, a matsayinsu na fatan Majalissar ta 10, zasu zama manufofin da majalissar zata ɗora dukkan aiyukanta a kai.

Ya ce ɗaya daga cikin manyan manufofin majalissar shine samar da bunƙasar tattalin arziƙi da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗe, inda ya ƙara da cewa, yawan dogaron da Najeriya ke yi a kan fitar da mai ya jawo rauni ga tattalin arziƙin ƙasar.

A ganinsa, hanyar da za a bi domin magance matsalolin da sauƙa da tashin man fetur ke jawowa tattalin arziƙin Najeriya da kuma samar da ƙaƙƙarfan tattalin arziƙi ita ce, yin amfani da hanyoyin sanya hannun jari a ɓangarorin da ba na mai ba, kamar harkar noma, ƙere-ƙere da kuma sabbin hanyoyin samar da makamashi.

NAN

Comments
Loading...