For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissar Wakilai Ta Amince Da Kasafin Kudi Na 2022 Ta Kuma Mayar Da Shi Naira Triliyan 17

Majalissar Wakilai ta amince da kudirin dokar kasafin kudi na shekarar 2022.

Majalissar ta kara yawan kudadaden cikin kudirin dokar da gwamnatin tarayya ta mika mata na Naira Tiriliyan 16.39, inda majalissar ta mayar da shi sama da Naira Tiriliyan 17.

Amincewa da kudirin ya biyo bayan la’akari da rahotonnin da Kwamitin Kasafin Kudi da Kwamitin Kudi suka bayar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa Naira Tiriliyan 17.1 ya saba da Naira Tiriliyan 16.39 wanda majalissar zartarwa ta kasa ta gabatar.

Majalissar ta kara yawan hasashen kudin siyar da danyen mai zuwa dala 62 daga dala 52 kowacce ganga.

Yayin da majalissar ta tabbatar da hasashen canjin dala a kan Naira 410.15 kamar yanda shugaba Buhari ya gabatar mata.

Comments
Loading...