For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissar Wakilai ta Amince Da Kudirin Kulawa Da Lafiyar Yara Kyauta

Majalissar Wakilai ta Najeriya ta amince da kudirin dokar da zai tilasta gwamnatin tarayya samar da kiwon lafiya ga kananan yara kyauta a Najeriya a karatu na biyu.

Kudirin dokar da dan majalissar wakilai daga jihar Kebbi, Bello Kaoje ya gabatar an masa take da ‘Kudirin Samar da Dokar da za ta Tilasta Samar da Kulawar Lafiyar Dukkan Yara ‘Yan Najeriya Kyauta; Da Sauran Abubuwa Masu Alaka da Haka.’

Da yake jagorantar muhawara kan kudirin a ranar Laraba, Kaoje ya bayyana cewa, lafiyar yara na da bukatar kulawar da ta banbanta da ta manya.

“A tsari na halitta, yara suna girma da sauri, hakan kuma yana jefa su cikin hatsarin kamuwa da larurori da kuma cututtuka.” In ji shi.

Dan majalissar ya kuma bayyana cewa, “idan ba a gano matsalolin lafiya ana maganinsu, za su taba lafiyar yara a bangaren kwazo, halayya da kuma dabi’a” in da ya tabbatar da cewa “da temakon tsarin lafiya gwamnatin tarayya na Save One Million Lives, yana da matukar muhimmanci a mayar da kulawa da lafiyar yara kyauta a Najeriya.”

Comments
Loading...