For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissar Wakilai Ta Kafa Kwamitin Duba Dokar Zabe

Majalisar wakilai ta kafa kwamitin mutane bakwai kan kudirin gyaran dokar zabe, 2021.

Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, wanda ya sanar da kafa kwamitin a zaman majalisar na jiya, ya bayyana Adeyemi Raphael dan jam’iyyar APC daga jihar Ekiti, a matsayin shugaban kwamitin.

Kamar dai yanda Majalisar Dattawa ta yi, mambobin kwamitin majalisar wakilan guda biyar sun fito daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki. Ragowar ‘yan kwamitin biyu kuma sune yan Peoples Democratic Party (PDP).

‘Yan kwamitin sun hada da: Ahmad Abdullahi Kalambiana na APC, daga jihar Sokoto, Blessing Onu na APC, daga jihar Benue, Emeka Chris Azubogu na PDP, daga Anambra, Unyime Idem na PDP daga jihar Akwa Ibom, Abiodun Faleke na APC, daga jihar Lagos da Aishatu Dukku ta APC, daga jihar Gombe.

Kwamitin da majalisar dattijai ta kafa a makon da ya gabata yana karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye a majalissar, Abdullahi Yahaya na APC daga jihar Kebbi a matsayin shugaba.

Majalisun biyu sun muhawara kan sashi na 52 na kudirin gyaran dokar, wanda ke neman shigar da amfani da fasahar zamani a cikin tsarin zabe.

Sashe na 52 (3) ya yi tanadi don watsa sakamakon zabe ta hanyar na’ura daga mazabu.

Kwamitin hadin gwiwa na INEC wanda ya yi aiki a kan kudirin ya ba da shawarar cewa “Hukumar na iya watsa sakamakon zaben ta hanyar na’ura a inda da kuma lokacin da ya dace.”

Amma majalisar dattijai, yayin duba da nazartar kudirin, ta yi gyara a sashin “Hukumar (INEC) na iya yin amfani da na’urar sadarwa idan har hukumar sadarwa ta kasa NCC ta tabbatar da isasshe kuma amintaccen yanayin yin haka kuma majalissar kasar ta amince.”

A bayan dai, ‘yan majalisar daga PDP sun ba da shawarar yin kwaskwarima don bayar da cikakkiyar damar aiwatar da watsa sakamakon ta na’ura wanda mafi yawan’ yan majalisar APC suka yi watsi da shi, wanda hakan ya haifar da zama mai cike da rudani.

A wani zaman, James Faleke na APC, daga jihar Legas, ya ba da shawarar yin kwaskwarimar cewa “ana iya watsa sakamakon zaben ta hanyar na’ura da kuma ta mafani da hanyar da.”

‘Yan majalisar sun yi watsi da wannan a lokacin da aka kada kuri’a. Amma shugaban zaman, mataimakin kakakin majalisar, Idris Wase, ya yi nasarar dakatar da muhawarar inda hakan ya kai ga wani zagayen na hatsaniya a majalissar.

A cikin rashin samun jituwa, Majalisar ta yanke shawarar gayyatar jami’an Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) don yi mata bayanin halin da ake ciki na karfin sadarwar a duk fadin kasar.

Jami’an NCC sun yi bayanin cewa akwai takaituwar hanyoyin sadarwar a wasu wurare wanda hakan na iya hana watsa sakamakon ta hanyar na’urar.

Sun kuma ce babu wata hanyar sadarwa da ke da inganci 100%, saboda haka zai iya yiwuwa a samu kutse da magudi kan sakamakon da hukumar zabe ta tura ta hanyar na’urorin.

Bayan mika wannan ga majalisar, mambobin sun kasa cimma matsaya guda yayin da ‘yan majalisar daga bangaren PDP suka fice daga majalissar.

Daga baya majalisar ta zartar da kudirin tare da bayar da gargadi, inda ta bar INEC da zabin watsa sakamakon ta hanyar na’ura idan zai yiwu”.

Comments
Loading...