Wani kudirin doka da ke kokarin hana ‘yan Najeriya wadanda suka koyi aikin likitanci a kasar damar zama cikakkun likitoci har sai bayan sun yi wa kasar aiki na tsawon shekaru biyar ya tsallake karatu na biyu a jiya Alhamis.
Wannan na a matsayin hanyar magance yawaitar ficewar da likitocin Najeriya ke yi zuwa gurare masu gwabi, abin da ke kara durkusar da fannin lafiya a kasar.
Kudirin da Dan Majalisar Wakilai, Ganiyu Abiodun Johnson ya gabatar, an masa take da ‘Kudirin Doka Domin Gyara Dokar Aikin Likitoci ta Shekarar 2004’.
Ganiyu Abiodun ya ce, zai fi zama adalci ga likitoci, wadanda suka mori kudin ‘yan kasa a lokacin ta suke samun horo, da su bayar da tasu gudunmawar ga al’umma ta hanyar yin aiki a kasa na wasu ‘yan shekaru kafin su tafi wajen Najeriya aiki.
‘Yan majalisar da dama ne suka goyi bayan kudirin, sai dai an samu wasu da dama da suka bukaci da a sanya abin a matsayin zabi ga likitocin a sabuwar dokar.
Wani dan majalisa mai suna, Uzoma Nkem-Abonta ya ce, takura likita na tsawon shekaru biyar a Najeriya kafin ya fita neman aiki waje, kamar sanya shi a kangin bauta ne.