For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissar Zamfara Na Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu Gusau

Majalissar Dokoki ta jihar Zamfara ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Barrister Mahdi Aliyu Gusau.

Wannan na zuwa ne a ranar Juma’a lokacin da Babban Daraktan Hulda da ‘Yanjarida na majalissar, Malam Mustapha Jafaru Kaura ya fitar da sanarwa kan yunkurin.

Sanarwar ta ce, yunkurin ya samo asali ne daga bukatar yin hakan wadda Mataimakin Kakakin Majalissar, Nasiru Magarya ya gabatar ga majalissar.

Sanarwar ta cigaba da cewa, “Kamar yanda yake a sashi na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na Shekarar 1999, an baiwa ‘yan majalissun dokoki damar yunkurin tsige gwamna ko mataimakin gwamna kan zarge-zargen sabawa kundin tsarin mulki da wulakanta ofis.

“Saboda haka a yau, Mataimakin Kakakin Majalissar kuma Shugaban Kwamitin Kula da Binciken Kudi ya gabatar da kudirin tsige Barrister Mahdi Aliyu Muhammad Gusau daga matsayin Mataimakin Gwamnan jihar.

“Mataimakin Kakakin Majalissar na zargin Mataimakin Gwamna, Mahdi Aliyu Gusau da karya dokokin tsarin mulki, wulakanta ofis da kuma almundahana da kudade, wadanda duk laifuffuka ne da za su jawo tsigewa, inda ya kara da cewa, Sashi na 188 na kundin tsarin mulki na shekarar 1999 ya bayar da damar tsige mataimakin gwamnan ba tare da jinkiri ba.”

Da yake amsar kudirin, Kakakin Majalissar ya yi alkawarin cewa, majalissar za ta yi duba zuwa zarge-zargen a kan mataimakin gwamnan tare da daukar matakin da ya dace gwargwadon tanade-tanaden kundin tsarin mulki. (NAN)

Comments
Loading...