For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majalissu Tarayya Sun Amince Da Gyaran Tsarin Zaben Fidda Gwani, Za Su Mikawa Buhari Domin Ya Sa Hannu

Majalissar Tarayya, a ranar Talata ta amince da gyaran dokar zabe a karo na biyu bayan an samu amincewa da bin tsarin maslaha a wajen fidda gwani.

Haka kuma Majalissar ta sanya sabbin ka’idoji ga ‘yan-takara da kuma jam’iyyu domin shiga zabe.

A makon da ya gabata ne dai majalissun biyu suka sake duban Kudirin Gyaran Dokar Zabe, musamman sashin da yai magana kan zaben fidda gwanaye.

Wannan kuwa ya biyo bayan kin amincewa da gyaran dokar da Shugaba Buhari yai, saboda a ikirarin sa, an yiwa tsarin demokradiyya hawan kawara ta hanyar bayar da zabi daya kacal a maganar zaben fidda gwani – abinda ya ce ba zai taba amincewa ba.

To sai dai kuma a yunkurin majalissun na sake mayarwa shugaban kudirin dokar domin ya amince, sun yi kokarin bayar da zabi ga jam’iyyu a maganar zaben fidda gwanaye, wanda hakan ma ya zo da sabani a tsakanin abin da majalissun suka amincewa a makon jiyan.

Kwamitocin samar da daidaito a tsakanin majalissun sun zauna a ranar Litinin da ta gabata domin fitar da matsaya iri daya a kan batun.

Bayan wannan zama, majalissun sun samu daidaitar ra’ayi kan abinda za su mikawa Shugaban Kasa domin ya sanya hannu gyaran dokar ya tabbata.

A yanzu dai Majalissar Wakilai ta amince da tsarin maslaha wajen zaben fidda gwani, abinda a baya ta sabawa Majalissar Dattawa a kansa.

Haka kuma majalissun sun samun gamuwar ra’ayi kan tsare-tsare da ka’idojin yanda za a na gudanar da zaben fidda gwani a jam’iyyu.

KU KARANTA: INEC Da EFCC Za Su Kula Da Kashe Kudaden ‘Yan Takara A Zaben 2023

A yanzu Sashi na 84 yana cewa, “(2) Hanyar fitar da dan-takara a jam’iyya domin mukamai daban-daban dole zai kasance ta hanyar ‘yartinke, amfani da wakilai (delegates) ko kuma samar da maslaha tsakanin ‘yan-takara (consensus).

“(3) Jam’iyya ba za ta sanya tsari, ka’idoji ko dokokin yarda ko rashin yarda da dan-takara ba, a kan kowanne dan-takara a zabe, sai kamar yanda ya kasance a sashi na 65, 66, 106, 107, 131, 137, 177 da kuma 187 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka sabunta).”

A kan tsarin ‘yartinke, Sashi na 84(4) yana cewa, “Jam’iyyar da ta zabi yin amfani da ‘yartinke wajen fidda gwani, ta tabbatar ta baiwa dukkanin ‘yan-takara dama iri daya wadda za ta sa duk ‘yan jam’iyya su yanke hukunci kan zaben su, haka kuma dole a bi tsarin da aka zayyana a kasa:

“(a) A zaben fidda gwani na dan-takarar Shugaban Kasa, duk masu rijista da jam’iyya za su zabi ‘yan-takarar da suke so a guraren da aka ware a dukkanin mazabun da ke fadin kasa.

“(b) Hanyar da take sakin-layi na (a) a sama da wannan sashi ita za a bi wajen amfani da ‘yartinke a zaben fitar da gwani na ‘yan-takarar gwamna, majalissar dattawa, majalissar wakilai da kuma majalissar dokoki ta jihohi.

“(c) Za a hada Taron Jam’iyya na musamman domin tabbatar da dan-takarar da yake da mafi rinjayen kuri’u a zaben da aka gudanar a mazabu a matakin kasa, jiha, mazabar dan majalissar dattawa, mazabar dan majalissar wakilai da mazabar dan majalissar dokoki ta jiha kamar yanda ya faru.

Game da ‘yan-takarar da za su fito ta hanyar amfani da maslaha, Sashi na 84(9) ya ce, “(a) Jam’iyyar da ta zabi tsarin samar da maslaha dole ta nemi rubutacciyar amincewar duk ‘yan-takarar da suka nemi takarar a wannan mukami, suna nuna janyewarsu a takarar da kuma goyon bayansu ga dan-takarar da aka zaba a dalilin maslahar.

“(b) A yanayin da jam’iyya ta kasa samun amincewar dukkanin ‘yan-takara a rubuce saboda samun dan-takara na maslaha, dole ne ta koma ta yi amfani da ‘yartinke ko wakilai (delegates) domin fitar da dan-takara na wannan mukami.

“(c) Za a hada Taron Jam’iyya na musamman domin tabbatar da ‘yan-takarar da aka zama ta hanyar maslaha a kasa, jiha, mazabar majalissar dattawa, mazabar majalissar wakilai da mazabar majalissar jiha kamar dai yanda ya gudana.”

Comments
Loading...