Daga: Kabiru Zubairu
A yau Laraba ne Majalissun Tarayyar Nigeria da suka hada da Majalissar Dattawa da kuma Majalissar Wakilai suka sabunta matsayarsu game kudirin gyaran dokar zabe.
A baya dai Majalissun biyu duk sun amince da cewar, kowacce jam’iyya dole ne ta gudanar da zaben fidda gwani ta hanyar baiwa kowanne mai dauke da katin jam’iyya damar zabar gwanin da zai wakilci jam’iyyarsa a zabe, abin da ake kira da ‘yar tinke.
Wannan shine bangaren da ya jawo cece kuce tsakanin ‘yan siyasa, gwamnoni da kuma masu sharhi kan al’amuran yau da kullum, haka kuma, wannan shine sashin da ya janyo Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ki sanyawa dokar zaben hannu.
A yau Laraba, rana ta biyu bayan dawowar Majalissun biyu daga hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara, Majalissun sun yiwa kudirin gyaran dokar zaben kwaskwarima domin ya dace da abin da Shugaba Buhari ya nuna yana bukata.
A farkon watannan ne dai aka jiyo Shugaba Buharin na bayar da amsa da cewa, ba zai takurawa tsarin demokaradiyya ba, shi yasa bai aminta da zabin dama daya ba, ta aiwatar da zaben fidda gwani; haka kuma shugaban ya nuna cewar, matukar Majalissun suka cire wannan takurar to zai sakawa dokar hannu.
To sai dai kuma, a kokarin Majalissun biyu na sabunta dokar zaben, an samu sabani kan yanda kowacce Majalissa take ganin ya kamata a gudanar da zaben fidda gwanin.
Majalissar Dattawa
A zaman Majalissar Dattawa na yau Laraba, Shugaban Masu Rinjaye a Majalissar, Sanata Yahaya Abubakar daga jihar Kebbi, ya gabatar da kudirin sake duba kudirin dokar zaben.
Sanata Yahaya, a jawabinsa, ya tunawa majalissar dalilan Shugaba Buhari na kin sanyawa dokar zaben hannu wadda Majalissar Tarayya ta amince da ita a ranar Alhamis 18 ga watan Nuwamba, 2021.
Sanatan ya kuma bukaci Majalissar da ta janye hukuncinta kan sashi na 84 na gyaran dokar zaben, wanda ya jawo rasa sanya hannun Shugaban Kasa a dokar.
Da suke nuna amincewarsu da gyaran dokar, Dattawan sun gyara sashi na 84 wanda yai magana kan yanayin gudanar da zaben fidda gwani, inda a yanzu suka amince da zabin hanyoyi uku wajen gudanar da zaben fidda gwani a kowacce jam’iyya.
KU KARANTA: Majalissar Dattawa Ta Gabatar Da Kudirin Hana Karbar Kudin Haya Na Tsawon Shekara Sai Dai Wata-Wata
Zabuka ukun da Dattawan suka baiwa jam’iyyun sun hada da tsarin ‘yar tinke, tsarin amfani da wakilai (delegates) da kuma tsarin masalaha ko sasanto.
Haka kuma, Majalissar Dattawan ta yi gyara a sashi na 84(3) na dokar inda ta ce “duk jam’iyyar da ta zabi amfani da ‘yar tinke, to dole ne ta tabbatar da cewa an baiwa kowanne dan jam’iyya damar shiga zaben da kuma damar ‘yan jam’iyya su zabe shi, kamar yanda Mai Temakawa Shugaban Majalissar na Musamman, Dr. Ezrel Tabiowo ya sanar.
Ya kara da cewa, “sashi na 84(4) ya bayar da damar cewa, “duk jam’iyyar da ta zabi amfani da wakilai (delegates) a zaben fidda gwani dole ne ta bi hanyar da aka zayyana; (a) A wajen zabar dan takarar shugaban kasa, jam’iyya dole ta yi, (i) zaben cikin gida na musamman a kowacce jiha cikin jihohi 36 na kasa da kuma Babban Birnin Tarayya, inda za a baiwa wakilai (delegates) damar zabar dantakarar da yai musu a guraren da aka ware a manyan biranen jihohin a kuma ranar da aka ware.”
Sashin ya kuma bayar da damar yin Babban Taron Jam’iyya na Kasa wanda za a tabbatar da wanda ya fi samun kuri’u a jihohi a matsayin dantakarar jam’iyya.
Majalissar Wakilai
Ita ma a zamanta na yau Laraba, Majalissar Wakilai ta janye hukuncinta na sai dole kowacce jam’iyya ta yi amfani da ‘yar tinke wajen zaben fidda gwani.
‘Yan Majalissar sun canza zabinsu daga iya ‘yar tinke zuwa zabi guda biyu, zabin ko jam’iyya ta yi amfani da ‘yar tinken ko kuma ta yi amfani da wakilai (delegates) a zaben fidda gwanayenta.
Majalissar Wakilan ta banbanta da Majalissar Dattawa wajen bayar da zabin yin amfani da masalaha ko sasanto a matsayin hanyar samar da wanda zaiwa jam’iyya takara.