For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Majinyata Zasu Na Biyan Kuɗin Wuta A Asibitin Jami’ar Ibadan

Hukumar gudanarwar Asibitin Jami’ar Ibadan da ke Jihar Oyo ta sanya ya zama doka cewar, kowanne majinyaci a asibitin sai ya biya kuɗin lantarki naira dubu ɗaya a kullum.

Shugaban sashin mulki na asibitin, Wole Oyeyemi, ya sanar da haka a wata sanarwa da ya raba, inda ya ce, hukuncin ya biyo bayan tsadar wutar lantarki da kuma ta man dizel.

“Biyo bayan yawan ɗauke wuta a asibitin, tsadar kuɗin wuta, da kuma hauhawar farashin man dizel waɗanda suka gurgunta samuwar wutar lantarki, hukumar gudanarwa ta yanke hukuncin ɗaukar matakan rage matsalar rashin samuwar aiki yanda ya kamata a asibitin,” in ji Oyeyemi.

“A ƙarshe dai, na yi wannan rubutu ne domin na sanar da ku amincewar hukumar zartarwa na biyan kuɗin wuta naira 1,000 (dubu ɗaya) a kullum ga kowanne majinyaci da yake jinya a asibitin.

“Ana buƙatar da ku tabbatar da wannan tsarin nan da nan ba tare da ɓata lokaci ba.”

Jami’in Hulɗa da Jama’a na asibitin, Toye Akinrinola, ya faɗawa jaridar PREMIUM TIMES cewa, “akwai wasu abubuwa ma na kari game da hakan sama da abun da aka ga yana zagayawa”.

Ya ƙara da cewa, wasu ƴan kishin Najeriya sun fara temakawa asibitin da man dizel domin rage matsalar.

Comments
Loading...