For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Malaman Manyan Makarantu A Najeriya Sun Debe Kwanakin Shekaru 2 Suna Yajin Aiki A Shekaru 7 Na Mulkin Buhari

Malaman Jami’o’i, malaman polytechnics da na kwalejojin ilimi sun kwashe kimanin kwanaki 719 suna yajin aiki tun bayan fara shugabancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a watan Mayu na shekarar 2015.

Bincike kan yanayin aiki a manyan makarantun da jaridar PUNCH ta gudanar a jiya Laraba ne ya nuna hakan.

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU a yanzu haka tana tsaka da yajin aiki, inda take nuna fushinta kan gazawar gwamnatin Buhari na cika mata alkawuran da suka shafi walwalar malaman da kuma samar da wadatattun kudaden gudanar da jami’o’in da ma sauran abubuwa.

Haka ita ma Kungiyar Malaman Makarantun Polytechnics, ASUP, a ‘yan kwanakin nan ne ta kare yajin aikin gargadi da ta yi na tsawon makonni biyu.

Ita ma Kungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi, COEASU, a yanzu haka ta fara yajin aikin gargadi na wata guda.

Binciken ya nuna cewa, a watan Janairu na shekarar 2017, kungiyar ASUP, karkashin tsohon shugabanta na kasa, Usman Dutse, ta yi yajin aikin gargadi a tsakanin 30 ga watan Janairu zuwa 5 ga watan Fabarairu na shekarar.

Haka kuma, ASUU ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a ranar 17 ga watan Agusta na shekarar 2017 saboda dadaddiyar sa-toka-sa-katsin da ki ci ta ki cinyewa tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar.

Kungiyar ta janye wannan yajin aikin a ranar 17 ga watan Satumba na shekarar ta 2017.

‘Yan makonni bayan janye yajin aikin na ASUU, sai kungiyar malaman polytechnics, ASUP, ita ma ta fara nata yajin aikin a ranar 11 ga watan Nuwamba na shekarar 2017, inda ta debe kwanaki 15 tana yi sannan ta janye a ranar 29 ga watan na Nuwamba.

A shekarar 2018, malaman kwalejojin ilimi na kungiyar COEASU sun tsunduma yajin aiki a ranar 9 ga watan Oktoba, inda suka janye wannan yajin aikin a ranar 5 ga watan Disamba na na shekarar.

Haka kuma, a dai shekarar ta 2018, kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aikin watanni uku saboda gazawar Gwamnatin Tarayya na cika alkawura.

Wannan yajin aiki sai da ya tsallaka shekarar 2019, inda kungiyar ta ASUU ta janye shi a ranar 7 ga watan Fabarairu na shekarar 2019.

Haka ma dai, kungiyar ASUP ta malaman polytechincs ta fara wani yajin aikin ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2018, wanda ta janye shi a ranar 13 ga watan Fabarairu na shekarar 2019.

A shekarar 2020 ma, kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aikin gargadi na makonni biyu a watan Maris saboda gazawar gwamnati na aiwatar da alkawarin da gwamantin ta yi a shekarar 2019.

Wannan yajin aikin ya debe watanni 9 ba tare da gwamnati ta yi abun da ya kamata ba, da kuma matsalar annobar korona, abun da ya sa yajin aikin ya fi kowanne tsayi.

Kungiyar ba ta janye yajin aikin ba sai a watan Disamba na shekarar 2020.

Yayin da sauran kungiyoyin malaman manyan makarantu ba su shiga yajin aiki a shekarar 2021 ba, kungiyar ASUP ta yi yajin aikin kwanaki 65 a shekarar.

ASUP din ta fara yajin aikin a ranar 6 ga watan Afirilu, inda ta kawo karshensa a ranar 9 ga watan Yuni na wannan shekara ta 2021.

Yanzu haka a wannan shekarar da muke ciki ta 2022, yayin da kungiyar malaman kwalejojin ilimi ta COEASU ta sanar fara yajin aikin gargadi na makonni hudu, kungiyar malaman polytechnics ta kammala na ta yajin aikin na makonni biyu, inda kungiyar ASUU kuma ta ke cikin kwana na 122 tana nata yajin aikin.

Wannan yanayi dai ya matukar gurgunta harkar ilimin manyan makarantu a Najeriya, inda dalibai ke fuskantar gagarumin kalubale game da gobensu.

Comments
Loading...