Daga: Lukman Dahiru
Kungiyar manoman ridi ta jihar Sakkwato ta yabawa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal bisa gudunmawar da yake bawa kungiyar.
Yabon ya fito ne ta bakin shugaban Kungiyar Manoman Ridi ta jihar ta Sakkwato, Alhaji Shu’aibu Falke, a lokacin da aka kaddamar da tallafawa manoman ridi a jihar.
Falke yace, tun daga lokacin da gwamna Tambuwal ya shigo cikin al’amarin noman ridi aka samu cigaba a cikinsa a jihar.
Ya kara da cewa, gwamnan ya raba irin ridi da ya kai kilo 34,000, ya kuma bayar da kudi aka sayi injina guda 500, sannan aka sayi taki na ruwa dan leda guda 1,300,000, sai mashina guda 10.
Sakataren Kungiyar Samaila Gumbi, lokacin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, ya ce ” Kimanin tan 2000 aka samu na Ridi a wannnan shekara, a sakamakon tallafin da mai girma Gwamna ya bawa manoma a lungu da sako na kananan hakumomi 23 a fadin jihar nan, wannan ya sanya ‘yan kasuwa daga ko ina a fadin duniya ke tururuwar zuwa nan domin samun ingantaccen ridin da manomanmu suka samar”
A nasa jawabin, Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa, ya bayar da umarni ga kwamishinan Harkokin Noma da a bude damar yin rajista ga mutane masu bukatar noma domin raba dazukan jihar a rika yin noma.