For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Manufar Mustapha Sule Lamido Ga Fannin Noma (1)

Wannan bayanai ne game da manufar ɗan takarar gwamnan Jihar Jigawa a jam’iyyar PDP, Mustapha Sule Lamido a ɓangaren bunƙasa harkar noma, kuma ita ce manufa ta 7 cikin jerin manufofin ɗan takarar.

Manufata Ga Jihar Jigawa (Vll)

Zan fara da godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki waɗanda suke ta aiki ba dare ba rana don ganin mun ci gaba da kasancewa a kan turba mai kyau. A cikin ƴan makwanninan, muna ta gudanar da taruka da shugabanni da jagorori daga ƙananan hukumomi 27 na jiharmu domin ƙulla kyakkyawar fahimtar da zata bamu damar kyautata manufofinmu da yaɗasu ko’ina har zuwa mutanen dake ƙasa. Ina ƙara gode wa dukkan waɗanda suke bada gudunmawa a ƙashin kansu don ci gaban Jihar Jigawa.

Kwanakin baya, na samu ƙorafin cewa bamu zo da wani abu sabo ba tunda manufofinmu sun maida hankali kan matsaloli gama-gari irinsu ilimi, kiwon lafiya, noma, albarkatun ruwa da sauransu, waɗanda wasu abubuwa ne da kowanne shugaba a Najeriya yake tinƙahon yi. Gaskiya ni kaina ina da irin wannan takaici domin akwai damuwa sosai a ce bayan sama da shekaru 60 da samun ƴancin kai har yanzu Najeriya tana fafutukar ganin ta cimma irin waɗancan abubuwa. Wataƙila yanzu ya kamata a ce muna tattauna batutuwan ci gaban zamani irin na ƙarni na 21. To, amma ba a gini sai da fandisho, don haka dole sai mun gyara waɗancan abubuwa. Fatanmu shi ne nan da wasu shekaru mu wuce da batunsu Insha Allah.

Yau ina so mu tattauna harkar noma wanda a yanzu shi ne ƙashin bayan tattalin arzikin ɗaiɗaikun jama’ar Jigawa. Sama da 75% na mutanenmu manoma ne amma masu noma abincinsu kaɗai. Harkar noma tana da faɗi sosai ta yadda ba zaka iya bayaninta a taƙaice ba. Don haka, ƙudurorinmu ga sashen suna da faɗi ta yadda muka zaɓi mu gabatar dasu a muƙalu guda biyu. Babban burinmu shi ne mu ɗaukaka harkar noma, ta bunƙasa zuwa wata babbar sana’a ta yadda ba sai ta dogara da gwamnati ba. Muna so mu samar da yanayin da manoma zasu yi ƙarfin da zasu tsaya da ƙafafunsu kamar yadda kamfanomi suke. Cikin wasu shekaru, sai gwamnati ta zama ita take ƙaruwa da kuɗin shiga daga noma maimakon ware masa kuɗaɗe a kasafin shekara-shekara.

Farko dai mun yi sa’a domin Jihar Jigawa tana da dukkan abin da ake buƙata domin samun ci gaban noma. Faɗin ƙasarmu ya kai sakwaya kilomita 24,742, kuma kaso mai girma daga ciki ya dace da noma. Aune-aunen Hukumar Kula da noma da Raya Karkara ta Jihar Jigawa (JARDA) ya tabbatar da cewa muna da ƙasar fadama mai faɗin sakwaya kilomita 3,433.79 (14% na faɗin ƙasarmu gabaɗaya). Ƙari a kan wannan, muna da yawan matasa da masu jini a jika sama da miliyan 3.

Bayan sababbin tsare-tsarenmu ga harkar noma, muna da tanadin ɗorawa a kan nasarorin gwamnatin PDP ta baya. Muhimman abubuwan da muke son cimma sun haɗa da magance rikicin manoma da makiyaya, ɗaga darajarsa daga noma don abinci zuwa don kasuwanci ta hanyar amfani da injina, samar da jarin noman, zamanantar da noman da yinsa tare da ilimi ta hanyar bincike da farfaɗo da tsarin malaman gona, samar da tsarin noman rani mai inganci, zamanantar da kiwo da inganta asibitocin dabbobi, inganta tsarin adana kayan noma don kar su lalace da kuma sarrafasu, sauƙaƙa hanyar samun taki da kayan aiki da kuma samar da alaƙa ta aiki tsakanin noma da masana’antu.

Zamu fara da samar da haɗin guiwa da hukumomi a ciki da wajen Najeriya domin ɗora noma a kan tsari na zamani. Za mu yi aiki da ƙwararru domin duba yanayin ƙasar nomanmu da irin amfanin gonar da ta dace dasu saboda ba wa manoma shawara kan abubuwan da ya kamata su shuka a guraren da suke da kuma dabarun yin hakan. Wannan shi zai share mana hanyar komawa tsarin noma a kimiyyance. Zamu dinga auna gudunmawar da noma da ɓangarorinsa suke bawa tattalin arziƙinmu lokaci lokaci domin gane ci gaban da muke samu.

Daga cikin ƙudurorinmu shi ne ƙarfafa guiwar ma’aikatan gwamnati da kamfanoni su shiga harkar noma a matsayin ƙarin sana’a. Gwamnatinmu zata duba yiwuwar ware wasu kuɗaɗe don bada rancen yin noma ga ma’aikata ba tare da kuɗin ruwa ba wanda za a dinga cirewa daga albashinsu a tsawon wani lokaci. Waɗanda aka tabbatar suna kan tsarin noman ne kaɗai za a ba wannan rance.

Zamu samar da ingantaccen tsari mai ɗorewa don tallafa wa manoma da hanyar samun jari. A ƙarƙashin tsarin Anko Borowa na Gwamnatin Tarayya, an rawaito cewa Babban Bankin CBN ya raba sama da naira biliyan 5 ga manoman Jigawa tsakanin 2016-2021. Amma da wahala mu iya auna takamaiman tasirin wannan tsari kan ci gaban noma a jiharmu tunda yawanci ba manoman gaske bane suke mora. Zamu haɗa guiwa da Gwamnatin Tarayya domin cire siyasa daga irin wancan rance da ake bayarwa ta yadda manoman gaske ne kaɗai zasu samu ba tare da nuna bambancin ra’ayin siyasa ba. Daga nan sai mu faɗaɗa tsarin, mu inganta shi ta hanyar sa idanu da bibiya Insha Allahu.

Zamu farfaɗo tare da inganta tsarin malaman gona ta hanyar shigar da masu digirin noma cikin tsarin. Zamu basu horarwar da ta dace domin su laƙanci dabarun noma na zamani da yadda ake samun irin shuka da na dabbobi masu kyau domin koyawa manoma. Za a samar da malaman gona a ɓangaren gandun daji, noman zuma, kiwon kaji, kiwon kifi da sauran dabbobi.

Zamu yi nazari kan tsarin yadda manoma suke samun taki da kayan aiki a ɗaiɗaikunsu da kuma matakai na ƙungiya. Don tabbatar da samuwar taki a koyaushe kuma cikin farashi mai sauƙi, zamu gayyaci ƴan kasuwa domin zuba jari da gina kamfanunawan sarrafawa da haɗa takin zamani. Haka kuma zamu nemo masu zuba jari don samar da masana’antun maganin feshi, abincin dabbobi da sauransu, domin mu daina zuwa wasu gurare neman waɗannan abubuwa.

Ba zamu je ko’ina ba idan bamu musanya fartanya ko garma da motocin noma na zamani ba; amma muna sane da cewa manyan injina da motocin amfanin gona zasu lamushe kuɗaɗe sosai. Tunda zai yi wahala a samar dasu ga kowa a lokaci guda, zamu samar da tsarin karɓar aro ko haya. A ƙarƙashin wannan tsarin, za a samar da waɗannan kayayyaki a wasu garuruwa inda ƙungiyoyin manoma zasu dinga ara kuma za a koya musu yadda ake sarrafawa da kula da su tare da sanya idanun waɗancan malaman gona da muka ambata a baya.

Zamu ba wa noman rani muhimmanci sosai. Jigawa tana da dama damai guda 8, Dambo, Kazaure da Wawanrafi duk a Kazaure LGA, Warwade a Dutse LGA, Galambi da Hayin Walde a Gwaram LGA, Kafin Gana a Birnin Kudu LGA sai kuma Kalwai a Kaugama LGA. Insha Allahu zamu samar da ƙudurori domin cin moriyar waɗancan dama-damai. Nan gaba, zan yi bayanai kan manufofi da tsare-tsarenmu kan Fulani makiyaya, kiwon dabbobi, tsarin adana kayan gona, sarrafasu da cinikayyarsu da kuma duk sauran abubuwa masu alaƙa da hakan.

Gobe ta Allah ce
©Santurakin Dutse

Comments
Loading...