Wannan bayanai ne game da manufar ɗan takarar gwamnan Jihar Jigawa a jam’iyyar PDP, Mustapha Sule Lamido a ɓangaren bunƙasa harkar noma, kuma ita ce manufa ta 8 cikin jerin manufofin ɗan takarar.
Manufata ga Jihar Jigawa (VIII)
Kwanaki kaɗan baya muka kammala tarukan ganawa da masu ruwa da tsaki inda muka tattauna da shugabanni da mabiyan jam’iyyarmu a faɗin ƙananan hukumomi 27 na jiharmu. A cikin makwanni huɗu, mun karɓi shawarwari masu nagarta daga wakilan jama’a. Bayan godiya ga dukkan waɗanda suka sadaukar da lokacinsu don ganawar, ina tabbatar muku da cewa zamu gudanar da gwamnati mai tafiya da kowa idan mun samu nasara. Duk da wahalar dake tattare da hakan, muna yin iya ƙoƙarinmu wajen ganin an saurari koken kowa a cikin wannan tafiya; amma iyawa kowa sai Allah.
Yau, ina so mu kammala tattaunawar da muka fara kan fannin noma. Abu muhimmi da ya kamata mu yarda da shi shi ne noma ba zai samu ci gaba ba a ƙarƙashin tsarin kai-kaɗai-gayya ba. Dole sai manoma sun dunƙule waje daya domin taimakon aiyukan junansu. Akwai buƙatar a farfaɗo da ƙungiyanci ba wai don a haɗu a cimma wata manufar siyasa ta lokaci ɗaya kawai a watse ba, a’a sai don a dinga musayar fasaha da dabarun inganta noma a tsakanin juna.
Ɗaya daga cikin matsalolinmu shi ne amfani da irin shuka mara inganci wanda yake sanadaiyyar rashin samun amfanin kirki. Domin magance wannan, muna da burin shiga haɗin guiwa da cibiyoyin bincike kan fannin noma kamarsu ICRISAT, IITA, IFAD da hukumar iri ta ƙasa (NSC) domin samar da gonakan gwaji wanda za a gamsar da manoma kan ingancin irin da za a raba musu. Ko shakka babu wannan zai haɓɓaka yawan amfanin gonar da muke samu.

Yanzu haka mun ɗauki nauyin wani bincike wanda ya tattara sahihan bayanai kan dukkan amfanin gonar da ake shukawa a Jigawa a kowacce ƙaramar hukuma da garuruwa. A dunƙule,. Zamu iya cewa abubuwa biyar da aka fi nomawa su ne shinkafa, zoɓorodo, riɗi, dawa da gero. Waɗannan kayayyaki ne da ake iya fitar dasu ƙasashen waje kuma ake amfani da su a masana’antu. Haka kuma muna da nau’ikan dabbobi da suka haɗa da tumaki, akuyoyi, shanu, raƙuma da kaji waɗanda suke samar da nama, madara, fata da ƙirgi.
Muna da burin ɓullo da sababbin ƙudurori a kan kiwon dabbobi musamman wajen inganta iri na dabbobin da lafiyarsu. Kamar ƴan Adam, dabbobi ma suna buƙatar kulawa da ingantaccen kiwon lafiya. Don tabbatar da haɓɓaka harkar kiwo, Insha Allahu zamu gyara asibitocin bitnariya tare da gina sababbi. Zamu ɗauki likitocin dabbobi da malaman kiwo domin inganta lafiyar dabbobi a jihar.
Zamu kawo tsarin inganta alaƙa tsakanin manoma da makiyaya tare da kawo dauwamammen zaman lafiya a tsakaninsu. Insha Allahu zamu tabbatar da sake fitar da burtalai da farfaɗo da waɗanda aka cinye tare da samun wasu kilatattun gurin kiwo. Waɗannan na daga cikin irin aiyukan PDP na shekarar 2007 zuwa 2015 wanda yayi maganin kusan bakiɗayan rikicin makiyaya da manoma, amma yanzu an yi watsi da wannan tsare-tsare.
Daga cikin matsalolin da suka haifar da wannan rikici har da hanƙoran manoma na su ƙara yawan gonakansu don samun amfani mai yawa. Kasancewar muna da burin inganta hukumar bincike kan fannin noma ta Jihar Jigawa musamman ɓangaren samar da ingantaccen irin shuka, manoma zasu dinga samun amfani mai yawa a guri kaɗan. Idan aka samarwa da makiyaya gurin kiwo da burtalai domin wucewa, za a samu warakar wannan rikicin.

Akwai wasu nau’ika na noma waɗanda bamu damu dasu ba kuma suna kawo kuɗi da riba mai yawa a wasu gurare. Abubuwa kamar kiwon kifi, noman ƴaƴan itatuwa, noman zuma, noman fulawoyi da sauransu, duk muna ganin kamar baza mu iya yi ba ko yankinmu bai dace da su ba. Idan aka nemo ƙwararru, zasu iya bada shawarwari da hanyoyin da suka dace wajen yinsu a yanki irin namu.
Zamu iya inganta manyan kasuwanninmu da yi musu gyaran fuska domin su ƙara zamantowa cibiyoyin cinikayyar kayan gona na zamani. Kasuwar Maigatari ta shahara kan dabbobi inda ake zuwa saye har daga wasu ƙasashe, Gujungu babbar kasuwa ce da ake sayar da kusan dukkan nau’in kayan gona, hatsi da dabbobi. Hakazalika kasuwar Sara a ƙaramar hukumar Gwaram, Shuwarin a ƙaramar hukumar Kiyawa da Kasuwar Kafin Hausa. Zamu iya amfani da waɗannan kasuwanni don ƙara bunƙasa cinikayyar amfanin gona.
Don samun ƙarin kasuwa, dole sai mun inganta tsarin ajiyar kayan gona don gudun lalacewa da asara, musamman kayan miya. Zamu bawa tsarin adana kayan gona muhimmanci tare da horar da manoma kan dabarun ajiya da rage asarar. Za a samar da rumbuna na zamani tare da haɗin guiwar hukumar bincike kan dabarun ajiyar amfannin gona ta ƙasa (NSPRI) da kukumar bincike kan sarrafa ɗanyen kaya (RMRDC) da ma sauran hukumomi kan wannan al’amari. Zamu duba yiwuwar kafa cibiyoyin sanyaya kaya don hana lalacewar kayan gwari a kowacce shiyyar majalisar dattawa guda uku da muke dasu.
Kamar yadda muka faɗa a baya, burinmu shi ne samun ci gaba daga noma don abinci zuwa noma don kasuwanci. A dunƙule, muna so mu ƙulla alaƙa tsakanin noma da haɓɓakar tattalin arziki wanda zai buɗe hanya zuwa ga sama wa dubban jama’a aiyukan yi. Babu wani sashen da yake da damar samarwa da miliyoyin jama’a kai tsaye ko ba kai tsaye ba hanyoyin dogaro da kai kamar noma.
Yayin da muke tattauna waɗannan manufofi, ya zama dole in bamu shawara kan mu yi duba izuwa abubuwan da kowannenmu ake buƙatar mu aiwatar kafin tabbatarsu a aikace. Lokaci ya wuce da gwamnati take da ƙarfin iya yin komai ita kaɗai. Koma bayan tattalin arziki yanzu ba zai bada damar yin abubuwa gabadaya ba. Jama’a, musamman manoma sai sun nuna sadaukarwa tare da goya wa gwamnati baya da ƙarfafar ta idan muna son noma ya cigaba. Amma abin jin daɗin shi ne idan mun samu nasara, zamu dinga bin abubuwa ne daki-daki sannu a hankali, kuma cikin taimakon Allah, komai mai yiwuwa ne.
Gobe ta Allah Ce
©Santurakin Dutse