Daga: Mustapha Sule Lamido
Zan fara da godiya da jinjina ga ƴan uwana mutanen Jihar Jigawa bisa fitowa da suka yi domin kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen shugaban Ƙasa da na ƴan Majalisun Tarayya. Duk da irin ƙalubalen da aka fuskanta, mutane sun nuna haƙuri wajen bin layi don zaɓo waɗanda zasu jagoranci ƙasarmu. To amma duk da haka, ina ganin akwai buƙatar mu ƙara himma wajen fitowa a zaɓuka masu zuwa. A cikin mutane masu rajistar zaɓe miliyan 2.35 da muke dasu a Jigawa, ƙasa da miliyan ɗaya ne kaɗai suka kaɗa ƙuri’a a zaɓen Ranar Asabar da ta gabata wanda hakan bai fi 40% ba.
Zan yi amfani da wannan dama don taya murna ga ƴan takarkarin Jam’iyyar PDP na Jiharmu da na sauran sassan ƙasarnan waɗanda suka samu nasarar lashe zaɓe a matsayin sanatoci da ƴan majalisu. Ina kira garesu da su mayar da hankali kan manufofi da tsare-tsaren da zasu taimaki jama’a waɗanda aka san jam’iyyar PDP da su. Muna kira ga Hukumar INEC da jami’an tsaro su yi gyare-gyare da ƙara shiri don ɗinke ɓaraka da magance kura-kuren da suka haddasa maguɗin da ya sa Jam’iyyarmu ta rasa wasu kujerun ƴan majalisu a Jihar Jigawa da sauran gurare a saasan ƙasarnan.
Game da zaɓen shugaban Ƙasa, mutane da yawa sun tofa albarkacin bakinsu a kan wasu muhimman al’amura masu alaƙa da doka da shari’a. Na san cewa shugabanni da jagororin Jam’iyyarmu na ƙasa sun yi nazari sosai a kan abubuwan domin ɗaukar matakin doka da ya dace. Ni daga ɓangarena, ina kira ga jama’a su zauna lafiya, su zama masu bin doka kuma su sanya idanu sosai tare da kyautata zaton gyaruwar al’amura. Kada mu karaya, mu ci gaba da jajircewa da yin aiki don samun ƙasa ta gari a 2023 da kuma gaba.
Ina miƙa godiya ta ga dukkan masu ruwa da tsakin Jam’iyyar PDP na Jihar Jigawa bisa aiki tuƙuru da suka yi a zaɓen shugaban Ƙasa da kuma rashin nuna gajiyawa wajen bada gudunmawa a tsawon watanni shida da suka wuce. Ba shakka, kun nuna sadaukarwa, jajircewa da amana. Irin wannan jajircewar taku ce ta taimaka wa PDP wajen cimma nasarorin aiwatar da daki-barin aiyyuka a shekarun 2007-2015 da har yanzu ba a kamanta irinsu ba a Jihar Jigawa. Zamu ci gaba da dogaro kan gudunmawarku don tabbatar da samun nasara a zaɓen Gwamna da ƴan majalisun jiha.
Kasancewar mun kewaya dukkan ƙananan hukumomi 27 domin gabatar da manufofinmu ga jama’ar Jihar Jigawa, bana jin akwai buƙatar sake maimata tsare tsarenmu a yanzu. Mun riga mun fitar da kundin manufofinmu tun watan Nuwamba wanda muke ci gaba da karɓar shawarwarinku game da shi. Zamu yi masa gyaran fuskar da ya dace da muradunku inda buƙata kuma zamu yi iya bakin ƙoƙarinmu wajen aiwatar da shi idan kuka bamu dama Insha Allah. Muna kira da mata, matasa da dattawa su bamu goyon bayan da muke buƙata.
Yau ina so na maida hankali kan yin cikakken bayani a kan abubuwa guda uku masu matuƙar muhimmanci kafin zaɓe. Na farko, ina shaida wa kowa cewa ina fatan zama gwamna kuma hadimin haɗaɗɗiyar Jihar Jigawa, bai wai gwamnan wani ɓangare ko wasu wararrun mutane ba. Na sha faɗa cewa, haɗin kan Jigawa shi ne abu na farko a cikin manufofinmu, a taƙaice ma dai shi ne babban dalilin da yasa na shiga wannan takara. Idan na zama gwamna, zan yi wa kowa adalci Insha Allahu. Don haka ina kira ga dukkan masu ɗabbaka siyasar ɓangaranci da niyyar taimakonmu ko cutar damu, su daina. Jihar Jigawa ba zata taɓa kai wa inda take so ba a matakin ci gaba da rarrabuwar kai. Don haka, ya zama dole mu fahimci mummunan tasirin waɗannan abubuwan da muke yi.
Na biyu, ina jaddada cewa na shirya wa wannan aiki. Idan ina tunanin ba zan iya ba, ba zan shiga wannan takara ba. Mun riga mun tsara dukkan abubuwan da muke so mu cimma tun daga ranar farko, kuma Insha Allahu ba zamu yi wasa ba. Zamu ɗauki kowacce rana a gwamnatinmu da matuƙar muhimmanci. Mun riga mun samar da abokan aiki da haɗin guiwa da muke buƙata. Ina tabbatar muku, ba zamu baku kunya ba idan kuka bamu dama. Zamu saurareku kuma zamu yi aiki don inganta rayuwarku. Muna da yaƙinin ba zaku yi nadamar zaɓarmu ba Insha Allah.
Na uku, ina kira ga jama’ar Jihar Jigawa su fita wajen kaɗa kuria a ranar zaɓen gwamna da kishin Jiharmu a ransu. Mu sanya jiharmu a farko. Mun bawa APC shekaru 8 kuma mun ga iya abin da zasu iya. Sun yi alƙawarin ɗorawa daga inda suka tsaya wanda hakan bai wadatar ba. Mu kuma mun yi alƙawarin kawo tsare tsaren da zasu ɗaukaka jiharmu fiye da yadda take a yanzu. Mu sa hikima wajen kaɗa ƙuri’unmu.
Mun fahimci cewa Jam’iyya mai mulki burinta shi ne maguɗin zaɓe. Muna ta karɓar rahotanni masu tada hankali kan yadda suke da niyyar yin amfani da hanyoyi daban daban domin juya sakamakon abin da mutane suka zaɓa. Wannan abin takaici ne duba da cewa masu yin hakan sune suka fi kowa cin moriyar ingantaccen zaɓe a baya. Da ana mana dariya ana ganin bamu isa ba, an manta cewa girma da ɗaukaka a hannun Allah suke, yanzu kuma so ake a turmushemu da ƙarfin tsiya. Ina kira a garemu mu tashi mu kare ƙuri’inmu kuma mu hanasu cimma mummunan ƙudurinsu. Mu yi watsi da duk wata barazana da zasu yi mana.
Duk wanda ya yi ƙoƙarin sayen ƙuri’unku da kuɗi ko kayan abinci, to ya nuna ƙololuwar rashin girmamawa gareku. Kawai yana ganinku a matsayin waɗanda zai iya amfani dasu a lokacin da ya ga dama. Ƙuri’unmu sun fi ƙarfin duk wani farashi. Kamata ya yi a ce mutanen da suka yi shekaru takwas suna mulki su burgeku da aiyukan raya ƙasa ba wai kyautar kayan abinci da kuɗin da baza su magance muku matsalolin da suka saka ku a ciki a shekaru huɗu masu zuwa ba.
Alhamdulillah, wannan doguwar tafiya tamu ta zo da ƙalubale iri iri. Amma dai ko sau ɗaya ban taɓa nadamar shiga siyasa ko tsayawa takara ba. Ina da yaƙinin cewar ba wani abin da zaka iya canzawa ba tare da ka shiga an dama da kai ba. Babu wasu kalamai da zan iya amfani da su wajen gode muku. kan irin soyayya, goyon baya da karɓuwa da kuka nuna mana. Zan yi alfahari da wannan har ƙarshen rayuwa ta. Ko yanzu mun kafa tarihi, domin mun gudanar da kamfen mai manufa wanda ya zama abin misali a tarihin siyasar Jihar Jigawa. Sannan kuma da goyon bayanku, zamu kafa wani tarihin Ranar Asabar, 11 ga watan Maris, 2023. Insha Allah.
Gobe ta Allah ce!
©Santurakin Dutse.