For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Manyan Arewa Ne Suka Ce A Zaɓi Atiku A PDP

Rahotanni sun baiya cewa, nasarar da Atiku Abubakar ya samu a daren jiya Asabar ta samo asali ne daga manyan ƴan Arewa.

Atiku ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP bayan ya samu ƙuri’u 371 inda Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya zo masa na biyu da ƙuri’u 237, yayin da tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Bukola Saraki ya zo na uku da ƙuri’u 70.

Gwamna Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom ya samu ƙuri’u 38; Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya samu ƙuri’u 20; tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Anyim Pius Anyim ya samu ƙuri’u 14; Sai kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar masu Haɗa Magunguna ta Najeriya, Sam Ohuabunwa, ya samu ƙuri’a ɗaya kacal.

An rawaito cewa, sanya bakin manyan Arewan ne ya sa Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da Muhammed Hayatud-Deen janyewa daga takarar.

Manyan sun gana da masu neman takarar Shugaban Ƙasar da suka fito daga Arewacin Najeriya ne a daren Juma’ar da ta gabata.

Manyan ƙarƙashin jagorancin tsohon Mai Bayar da Shawara na Kasa kan Lamuran Tsaro, Janar Aliyu Gusau mai ritaya da kuma tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa sun yi ganawa ta musamman da ƴan takarar da suka fito daga yankin Arewa domin rage yawansu zuwa guda ɗaya kacal.

Wata majiya daga wajen ganawar ta sanar da cewa, an buƙaci ƴan takarar na yankin Arewa da su janye su barwa Atiku, wanda suke ganin yana da karɓuwa a dukkanin faɗin Najeriya sama da sauran.

A lokacin zaɓen fidda gwani domin babban zaɓen 2019, an gano Janar Aliyu Gusau a Port Harcourt na Jihar Rivers yana faɗawa ƴan takara cewa, yana magana ne da yawun kafatanin manyan Arewa.

Ya baiyana cewa, Atiku zai fi dacewa wajen kulawa da ƙasa sannan kuma jam’iyya mai mulki da Gwamnatin Tarayya da ba su da abin faɗa a kansa wanda ba su faɗa ba.

Ya ce, manyan Arewa sun gamsu da cewa, babu wata hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da za ta tuhumeshi, sannan kuma ko ina a Najeriya an san shi.

Muhammad Hayatud-Deen ya nuna amincewarsa ta janyewa tun a lokacin, yayin da sauran ƴan takarar suka ce zasu yi tuntuɓa tukunna.

Majiyar ta ce, Tambuwal ya ce zai baiyana makomarsa a wajen taron fidda gwanin, yayin da sauran kuma suka ce zasu faɗawa magoya bayansu yanda ya kamata su yi.

Jim kaɗan bayan Tambuwal ya baiyana janyewarsa daga takarar, Atiku ya yi rubutu a shafinsa na Twitter cewa, matakin na Tambuwal abin san-barka ne.

Comments
Loading...